Mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar soji ta bakwai a Maiduguri Kanal Sani Usman shi ya sanar da sakin mutane 42 wadanda yace basa cikin kungiyar Boko Haram.
Yayin da mutanen suke tsare rundunar sojojin tayi masu binciken kwakwaf kuma ta tabbata ba 'yan Boko Haram ba ne. Bisa ga sakamakon binciken ya sa hukumar tsaro ta kasa ta bada umurnin sakinsu. Cikin mutanen, uku 'yan kasashen waje ne da suka hada da Chadi da Kamaru da Burkina Faso.
Sojojin basu sakesu hannu banza ba domin kowannensu an bashi nera dubu dari daya ya je ya kama wata sana'r yi. Daga bisani Kanal Sani Usman ya mikawa gwamnan Borno Kashim Shettima mutanen.
Bayan da ya karbi mutanen gwamna Shettima ya jawo hankalinsu akan bukatar su zama mutane nagari kana yayi alkawarin samar masu ayyukan yi. Ya kuma basu yadunan shadda. Yace za'a taimaka masu amma su yi imani su ji tsoron Allah idan ba haka ba kuma za'a sake kamasu.
Mutanen da aka sake sun yi matukar murna tare da godiya. Sun tabbatar cewa an taimaka masu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.