Wasu kusoshin gwamnati da manyan 'yan siyasa har ma da wasu sarakuna da ake ganin su ne iyayen al'umma sun fara kwashe iyalansu suna ficewa daga jihar.
Bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace garin Mubi aka ga manyan suna janyewa daga jihar lamarin da wasu suka ce abun takaici ne. Wasu sun ce a wannan lokacin ya kamata a ce su manyan suke taimakawa jama'a. To amma yau su ne suke kan gaba wurin barin jihar. A ganin wasu wannan nuni ne cewa babu shugabanci a kasar. Mutane sun ga manya-manyan jiragen sama suna fitar da iyalan manya. Idan shugabanni sun bar gari ina talaka zai shiga.
Amma duk da wannan ficewar wasu manyan jihar, sarkin Mubi Alhaji Isa Ahmadu wanda 'yan Boko Haram suka kwace masarautarsa tare da fadarsa da kuma canza sunan garin daga Mubi zuwa Medinatul Islam, yunkurin komawa garin ya keyi.
Jama'a da suka ji yunkurin sarkin sun ce sun ji dadi kuma yin hakan ya nuna yana son talakawansa kuma a shirye yake ya sadakar da ransa dominsu.
'Yan Boko Haram dake rike da garin sun fara tilastawa mutanen garin su bude shagunansu ko su soma fasasu. Suna aiwatar da shar'a tare da yanke hannayen wadanda aka yiwa hukuncin akan sun yi sata. Sun kama 'yan mata suna aurar dasu. Matan da mazajensu basa nan su ma sun aurar dasu. Gidajen da mutane suka bari suka ki komawa ciki sun zama nasu.
Sai dai 'yan kungiyar kato da gora da aka fi sani da Civilian JTF sun ce lokaci yayi da ya kamata matasan Adamawa su tashi su kwato garuruwansu daga hannun 'yan Boko Haram.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.