Hukumar kwastan tace tana cigaba da samun kudaden shiga kamar babu abun dake faruwa a kasar.
Hukumar ita ce ta biyu wajen samar ma Najeriya kudaden shiga bayan na albarkatun man fetur.
A wata ziyarar aiki da shugaban hukumar kwastan din na kasa ya kai Minna jihar Neja, Alhaji Abdullahi Dikko Inde ya shaidawa Muryar Amurka cewa duk da durkushewar harkokin kasuwanci a yankunan Maiduguri da Yola, sha'anin shigo da kaya bai shafi sauran iyakokin kasar ba. Dalili ke nan da hukumar ta samar da nera miliyan dubu arba'in da biyar a matsayin kudaden shiga ma Najeriya a wannan shekarar.
Rashin tsaro da tashin hankali a arewacin kasar sun jefa al'ummomi da dama cikin wani mawuyacin hali musamman jami'an tsaro. Jami'an kwastan na cikin jami'an dake tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasar.
Dangane da matsalar tsaro da hukumar ke fuskanta, Alhaji Abdullahi Dikko Inde yace komi ya ta'allaka ne akan adalcin shugaba. Yace su a hukumar kwastan sun tabbatar da yiwa yaransu adalci sabili da haka ya san yaransu zasu cigaba da yin kokari. Duk aikin da tsarin doka ya zana masu babu gudu ba ja da baya. Zasu tsaya su yishi yadda ya kamata. Ya kira kowane shugaba yayi adalci tare da jin tsoron Allah. Rashin adalci ne a tura yaro aiki ba'a bashi kayan aiki ba kuma a hanashi albashinsa kana a yi tsammanin zai tsaya ya dage a bakin aikinsa.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.