A ci gaba da kawo muku jerin hotunan bidiyon kan iri ta’asar da kungiyar Boko Haram ta yi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, a wannan karo za ku kalli hoton bidiyon mutumin da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka tafi mai da ‘ya’yansa mata.
Malamai da masana addinin Musulunci dake magana kan akidar tsageranci ko ta'addanci, sun ce Muslunci bai halalta daukar makami ba, sai idan mutum zai kare kansa ne. Haka kuma, addini yayi bayani dalla-dalla na abubuwan da hukumcinsu kisa ne.
Wadanda suka kai harin bam a Zabarmari lokacin bukin Sallah da kuma a Maiduguri, su na cika bakin wannan danyen aiki nasu. An kai hare-haren kunar-bakin-wake a Zabarmari a watan Yulin 2015. In har harin na kunar-bakin-wake ne, ta yaya wannan dan Boko Haram da suke kira Sheikh Tahiru yake daukar alha
Wani dan gudun hijira daga garin Kumshe da ya ga hotunan gine-ginen da aka ciro daga bidiyon kashe-kashe na 'yan Boko Haram, ya tabbatar da cewa lallai a garinsu aka aikata wannan abu. Duk da cewa bai ga hotunan kashe-kashen da aka yi ba, kuma bai ga hotunan 'yan Boko Haram rike da makamai ba, ya tu
A duk garin da 'yan Boko Haram suka kama a lokacin da suka mamaye wasu garuruwan arewa maso gabas a Najeriya, a shekarun 2014 da 2015, su kan kafa kotunan tafi-da-gidanka, su tattaro duk mutanen gari, babba da yaro, don yazo ya ga hukumcin da zasu yi. Wannan shine makaminsu na tabbatar da cewa kowa
Wasu daga cikin hotunan bidiyo na Boko Haram sun nuna wani matashi dan kungiyar yana sarrafa karamar jirgin saman "Drone" wanda aka makala kyamarar bidiyo ko hoto a jiki. An gansu zaune a kofar wani gida da ake kyautata zaton a ciki kwamandansu yake, suna gwada yadda jirgin ke tashi. Irin wannan jir
Ba a san takamammen inda aka dauki wannan hoton bidiyon ba, amma watakila kusa da Banki ne a Jihar Borno, inda sojoji da tankokin yaki na Kamaru suka taru, kuma masu leken asirin Boko Haram su na boye cikin ciyawa a kusa da su suna daukar hotunansu.
A wannan karon, suna boye cikin wata motar Jeep suna daukar hoton bidiyon kasuwar Kauyen Kulli dake karamar hukumar Mafa ta Jihar Borno, ba tare da mutane sun ankara da abinda ke faruwa ba. Muryar mai daukar hotonsu, Abu Umma, ko Abu Mama, ake ji a cikin wadannan bidiyon.
Ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya yaba da kokarin da VOA ta yi na nunawa duniya irin rashin imanin da 'yan Boko Haram suka rika nunawa a lokutan da suke rike da wasu sassan yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A garin Kumshe, an ga wani mutumin da aka zarga da laifin sayar da kwaya yana addu'a da kalmar Shahada jim kadan kafin 'yan Boko Haram su kashe shi (bidiyon Boko Haram).
Domin Kari