Boko Haram: Sarrafa Jirgin Saman "Drone"
Wasu daga cikin hotunan bidiyo na Boko Haram sun nuna wani matashi dan kungiyar yana sarrafa karamar jirgin saman "Drone" wanda aka makala kyamarar bidiyo ko hoto a jiki. An gansu zaune a kofar wani gida da ake kyautata zaton a ciki kwamandansu yake, suna gwada yadda jirgin ke tashi. Irin wannan jirgin "drone" ba irin wanda sojoji suke yin amfani da shi ba ne, karami ne wanda ake sayarwa a kasuwa mutane su na saya domin sha'awa. Ba a san ko amfanin me wannan "drone" yake yi musu ba.
Labarai masu alaka
Zangon shirye-shirye
-
Satumba 13, 2024
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Tabbatar Da Hallaka Halilu Sububu
-
Satumba 03, 2024
Mutum 129 Sun Mutu A Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yarin Congo
Facebook Forum