Wasu daga cikin hotunan bidiyo na Boko Haram sun nuna wani matashi dan kungiyar yana sarrafa karamar jirgin saman "Drone" wanda aka makala kyamarar bidiyo ko hoto a jiki. An gansu zaune a kofar wani gida da ake kyautata zaton a ciki kwamandansu yake, suna gwada yadda jirgin ke tashi. Irin wannan jir
Ba a san takamammen inda aka dauki wannan hoton bidiyon ba, amma watakila kusa da Banki ne a Jihar Borno, inda sojoji da tankokin yaki na Kamaru suka taru, kuma masu leken asirin Boko Haram su na boye cikin ciyawa a kusa da su suna daukar hotunansu.
A wannan karon, suna boye cikin wata motar Jeep suna daukar hoton bidiyon kasuwar Kauyen Kulli dake karamar hukumar Mafa ta Jihar Borno, ba tare da mutane sun ankara da abinda ke faruwa ba. Muryar mai daukar hotonsu, Abu Umma, ko Abu Mama, ake ji a cikin wadannan bidiyon.
Ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya yaba da kokarin da VOA ta yi na nunawa duniya irin rashin imanin da 'yan Boko Haram suka rika nunawa a lokutan da suke rike da wasu sassan yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A garin Kumshe, an ga wani mutumin da aka zarga da laifin sayar da kwaya yana addu'a da kalmar Shahada jim kadan kafin 'yan Boko Haram su kashe shi (bidiyon Boko Haram).
Bidiyoyin da kungiyar ta dauka ya nuno wani harin da suka kaiwa wani barikin sojoji a garin Banki. An faro bidiyon ne daga sa’adda mayakan suka taru da safe tare da shugabanninsu suna shirin su je su kashe ko a kashesu. Harin dai ya yamutse inda har su mayakan suka koma ihu suna rokon a basu makami.
Wani mayakin Boko Haram yana takawa ta cikin garin Banki a yayin da 'yan tsagera suka kai farmaki a kan wani barikin soja dake garin (bidiyon Boko Haram).
A cikin kashi na hudu na rahotannin bidiyo na musamman kan Boko Haram, yau zamu ga irin barnar da aka yi a wannan yakin, musamman a Jihar Borno, da kokarin da ake yi na sake gina birane, garuruwa da kauyukan da aka lalata su baki daya.
A cikin kashi na uku na rahoton bidiyo a kan kungiyar Boko Haram, an ga alamun baraka a tsakaninsu bayan da wani manzo na Abubakar Shekau ya bayyana a Kumshe yana bayyana wasu malaman kungiyar a zaman munafukai, yayin da wasu sanannun malamai suka ce babu fahimtar addini a akida irin ta Boko Haram
A kashi na biyu na rahoton bidiyo na musamman kan Boko Haram, zamu ga yadda suke zama su shirya kai hare-hare, da irin wa'azin da ake yi wa mayaka, da yadda ake turo musu kwamandojin yaki daga wasu wurare, da yadda suke tafiyar da fada, da kuma irin abubuwan da su kan biyo bayan kai farmakinsu
Domin Kari