A kashin farko na shiri na musamman kan Boko Haram, hotunan bidiyon da suke dauka sun nuna yadda suke tsoratar da jama'a dopmin su yi musu biyayya. Zamu leka kotunsu a garin Kumshe, wanda suka sanya ma suna Dimashka (Damascus) a kusa da garin Banki a Jihar Borno.
A kalla ko karanta rahotanni na musamman na VOA Hausa dangane da faya-fayen bidiyon sirri na Boko Haram.
Sojojin Najeriya sun samu nasarar kora tare da yin barna ma 'yan Boko Haram da suka kai farmaki kan garin Dikwa na Jihar Borno cikin wannan makon.
Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wani mummunan hari a jihar.
Sojojin Najeriya na cigaba da farautar mayakan sa kan boko haram a dajin Sambisa da sauran wurare, tare da ceto wasu da 'yan kungiyar suka yi garkuwa da su.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin adadin rayukan da suka salwanta a lokacin rikin garin Zariya tsakanin sojojin Najeriya da mabiya Mazahabar Shi'a.
A jiya Lahadi ne rikicin da ya kunno kai tsakanin mabiya Shi’a da sojojin Nijeriya a ranar Asabar ya ci gaba har ya haifar da kame shugabansu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky da kashe wasu daga cikin mabiyansa da masu tsaron lafiyarsa da ma babban likitansu da kuma kakakin shi El-Zakzakin.
Jami'an 'yan sanda sun tsaya kusa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja, domin kula da kara tabbatar da tsaro.
Jakada Amurka Michael Hoza, ne ya mikawa Ministan tsaron kasar Kamaru.
Rahotanni daga janhuriyar Nijar sun bayyana cewa hukumomin kasar na kokarin mika wasu ‘yan boko haram ga hukumomin Najeriya bayan da aka shafe lokaci mai tsawo ana tsare da su a gidajen yari daban daban.
A farkon wannan shekara shugaba Muhammdu Buhari na Nigeria,ya baiwa rundunar sojan Nigeria wa'adin watan Disamba na murkushe yan kungiyar Boko Haram.
Domin Kari