Al'umar birnin Maiduguri na ci gaba da korafi kan irin mawuyacin halin da suka shiga tun bayan da aka saka dokar hana fita. Hakan kuma na faruwa ne bayan da rahotanni ke nuna cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun sake kwace garin Marte.
'Yan gudun hijira da kuma sojoji kusa da Maiduguri.
Sojoji a birnin Maiudugri, sun kafa dokar hana fita bayan wani hari da ake zargin ‘yan kungiyar Boko ne suka kai.
Kalubalen 'yan boko haram ba kasar Najeriya kadai ya shafa ba, makwabtan kasashe kamar su Chadi,Niger da kamaru suma duk suna fuskantar matsalar.
Tawagar gwamnatin Jihar Borno ta kai ziyara a sansanin 'yan gudun hijira dake Makohil a jihar Adamawa saboda yawancin wadanda sojoji suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram 'yan asalin jihar ne.
Hukumar ba da agajin gaggawan ta tarayya mai kula da yankin jahohin Kebbi da Zamfara da Sokoto, wato NEMA, ta ce mafi yawan ‘yan gudun hijran da aka maido su daga Jamhuriyar Nijar ‘yan asalin Jahar Kebbi ne.
Amurka ta ce za ta taimakawa yankin arewa maso gabashin Najeriya wajen yaki da ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram.
Yanzu haka a Najeriya ana ta kiraye-kiraye, kan yadda gwamnatoci za su tallafawa yara kanana da suka rasa iyayensu sakamakon rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Yayin da yake jawabi wakilin yace ya lura cewa yara da dama suna fama da rashin abinci mai gina jiki da rashin koshin lafiya da ciwon ido.
Rundunar tsaro ta STF tayi karin haske akan harin da wasu 'yanbindiga suka kai a yankin Barkin Ladi da ya yi sanadiyar asarar rayuka da dama.
An yi kwana bakwai ana taro a garin Kontagora da nufin lalubo bakin zaren matsalolin da suka yiwa masarautar katutu.
Domin Kari