A wata sanarwa ga manema labarai, DSP Haruna Mohammed kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a ofisoshin gundumar yankin ‘yan sandan a wadannan kananan hukumomin biyu, bayan haka sun lalata wasu kayan zabe. Ya kuma ce hadin guywar jami’an tsaro sun dukufa wajen farautar ‘yan bindigar.
Wasu mazauna garin Kirfi sun fadi cewa an gudanar da zabe lafiya sai dai ‘yan bindiga sun kona wata cibiyar zabe a karamar hukumar. Wannan lamari ya faru ne bayan zabe amma babu jami’an tsaro a wurin lokacin da abin ya faru, kuma ba a sami hasarar rai ko wadanda suka jikkata ba. Duk da cewa harkoki sun fara komawa daidai, har yanzu jama’a na zaman dar-dar a ta bakin wani dan garin.
Wani mazaunin garin Alkaleri da ba’a ambaci sunansa ba ya fadi cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum daya a wajen wata kasuwa kuma sun sawa wani ofishin 'yan sanda wuta amma an yi nasarar kashe wutar.
A halin da ake ciki, jiragen sama na can na shawagi a sararin samaniyar birnin Bauchi.