Yanzu haka dai hankali ya kwanta a yankunan Taraba, bayan wani hargitsi mai nasaba da sakamakon zaben gwamna a jihar inda aka sami hasarar rayuka da kuma kone-kone a garin Gyambu.
Fiye da gwamnoni 20 ne jam’iyyar APC ta samu bisa ga sakamakon zaben bana. Haka zalalika jam’iyyar ta sami gagarumin rinjaye a zaben kujerun majalisar dokoki a yawancin jihohi, inda ma jam’iyyar ta sami dari bisa dari a majalisun dokokin jihohin Sokoto da Kano.
A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar boko haram ne, suka shiga wata makarantar sakandare a garin Chibok dake jihar Borno suka sace wasu ‘yan mata guda 276.
Yau shekara daya ke nan cur da 'yan Boko Haram suka sace daliban makarantar 'yan mata a garin Chibok jihar Borno.
Ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 'yan kungiyar Boko Haram suka kai samamme a makarantar 'yan mata dake Chibok jihar Borno inda suka sace dalibai 279 kafin wasu su samu su kubuce.
Garin Gwoza na daya daga cikin garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram a kwana kwanan nan.
Janar Buhari yace gwamnatinsa zata duba batun take hakin bil Adama da ake zargin jami'an tsaro da aikatawa
Da misalin karfe takwas na daren jiya wasu suka sace Baraden Wamako Alhaji Salihu Barade a gidan gonarsa.
Bayan kwashe watanni da dama a hanun 'yan kungiyar Boko Haram, dajin Sambisa wanda ake mai kallon mafaka ce ga 'yan kungiyar ya koma hanun dakarun Najeriya.
Rahotanni daga jihohin Bauchi da Gombe na cewa an ga 'yan bindiga cikin motoci suna ratsa wasu garuruwa a jihar Bauchi da Gombe
Yau aka shiga rana ta biyu da ci gaba da kada kuri'u a wasu sassan Najeriya bayan da hukumar zabe ta kara wa'adin rufe rumfunan zabe zuwa yau lahadi.
Na’urar Card Reader na tantance masu kada kuri’a da zarar an sa hotun su ko kuma yatsunsu. Na’urar dai a zaben shekarar nan ta 2015 ne hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ta fara amfani da ita.
Domin Kari