Shugabannan sun yi wannan bayanin ne jim kadan bayan da hukumar zabe ta gama tantance su a mazabun su dake birnin Minna. Sun kuma yi kira da ‘yan Najeriya su amince da sakamakon da aka fidda na zaben ba tare da tada hankali ba .
Tsohon gwamnann jihar Kano kanal Sani Bello mai ritaya da aka tantance shi a mazabar shi dake Kwantagora, shi kuma yayi kira ga ‘yan takara da su jawa magoya bayansu kunne su zauna lafiya don shine muhimmin abu a yanzu haka.
Dumbin jama’a sun yi cincirindo a rumfunan zabensu tun da sanyin safiyar yau Asabar don jiran hukumar zabe ta tantance su. Sai dai a wasu mazabun an sami dan tsaiko sakamakon na’urar nan ta tantance katin zabe da ake kira Card Reader a turance.
Su ma mata ba a bar su a baya ba wannan karon, sun fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri’a.
Kawo yanzu dai hukumar zaben jihar ta Neja bata yi wani Karin haske ba akan matsalar da ta hana yin zabe a wasu rumfunan zabe ashirin dake kananan hukumomi shidda dake jihar Neja.