Rundunar mayakan sojan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane goma sha hudu da kuma wasu ashirin da tara da suka sami raunuka, sakamakon tashin boma bomai da ya auku a cikin garin Maiduguri.
Bayanai daga Jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa ana samun karuwar yawan mutanen da suka mutu a hare-haren bam da aka kai a birnin Maiduguri.
A daidai lokacin da sojoji ke ikirarin samun galaba kan 'yan kungiyar Boko Haram a yakin da su keyi sai gashi 'yan ta'adan na kara yawan tada bamabamai cikin Maiduguri da kewaye
Biyo bayan bam da ya tashi a sansanin 'yan gudun hijira a Yola jihar Adamawa shugaban Najeriya ya bada umurnin karfafa tsaro a sansanin.
Rikicin kailanci da na addini na neman zama ruwan dare gama gari a jihar Taraba inda wasu sun yaudari wasu shugabanin al'umm daga bisani suka hallakasu.
Bayan sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta bayar na sake kwato garin Gamboru Ngala daga hannun Boko Haram mazauna yankin sun bukaci gwamnati ta gina barikin soja na din din din din a garin
Jiya rundunar sojin Najeriya ta sanarda sake kwato garin Gamboru Ngala daga kungiyar Boko Haran
Yau da safe aka samu tashin wasu tagwayen bamabamai a birnin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe.
Wasu da ba tantance ko su wanene ba sun kai hari garin Kotse dake jihar Taraba
Makon da ya gabata ne aka sanarda duniya cewa an samu canjin shugabancin kungiyar Boko Haram
Shugaba Idris Deby na kasar Chadi yace da alamun wani mai suna Mahamat Daoud shine ya maye gurbin Abubakar Shekau a matsayin shugaban kungiyar Boko Haram kuma yana son a yi tattaunawar sulhu da gwamnatin Najeriya
Dubun daubatan mutanen rikicin Boko Haram ya daidaita. Taimakon da gwamnati da wasu kungiyoyi suka shirya na tallafa masu wasu na ji ne kawai basu gani a kasa ba.
Domin Kari