Kawo yanzu da muhukunta sun tabbatar da mutuwar mutane biyu a harin da aka kai garin Kotse. Mutane biyar kuma sun amu munanan raunuka.
Har yanzu dai ba'a san ko su wanene suka kai harin ba kodayake kungiyar Boko Haram ta dade tana kai hare-hare a jihohin Borno da Adamawa da Yobe kuma rikicinkabilanci da na addini ya yiwa Taraba katutu.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansandan jihar DSP Joseph Kwaji ya tabbatar da aukuwar lamarin. Yace rundunarsu ta gano gawarwakin mutane biyu dukansu 'yan gida daya. Daya cikinsu an yi masa yankar rago a wata tsohuwar rijiya dake garin.
Wai mutane bakwai ne daga gida daya suka fita zasu je kogi kamun kifi sai wasu 'yan bindiga suka kai masu hari. Biyar sun samu sun arce amma sun kama biyu wadanda suka hallaka.
Wani mazaunin garin Hama Joseph yace rabonsu da samun irin wannan harin shekara daya ke na. Hankali ya kwanta yanzu amma mutane na fargaban fita zuwa gonakansu sakamakon harin.
Har yanzu dai babu wanda 'yansanda suka kama dangane da harin. Saidai abun takaici shi ne mutane biyun da suka mutu suna cikin wadanda suka koma garinsu daga gudun hijira sakamakon tashe-tashen hankula da yankin ya yi fama dasu. Mutanen sun koma jihar ta Taraba ne biyo bayan kiran da gwamman jihar ya yi cewa su koma domn su sake gina muhallansu saboda zaman lafiya da suka samu.
Ga rahoton Sanusi Adamu.