Garin Gamboru Ngala dake kan iyaka tsakanin Najeriya da kasar Kamaru ya kwashe fiye da shekara daya yana hannun 'yan Boko Haram. Da an fatattakesu sai kuma su sake komawa garin saboda yawa janyewar sojoji.
Ko lokacin da sojojin Najeriya suka yi ikirarin cewa babu wani gari dake hannun Boko Haram kungiyar ta fito fili ta karyata ikirarin tana cewa garin Gamboru Ngala a lokacin yana hannunsu.
Amma a wannan karon daraktan dake kula da hulda da jama'a na sojojin Najeriya Kanal Sani Shehu Usman Kukasheka shi ya fitar da sanarwar da ya aikawa manema labarai inda ya tabbatar rundunarsu ta sake kwato garin.
Ganin cewa wannan sanarwar ita ce ta biyu da sojojin suka yi Muryar Amurka ta zagaya inda 'yan aslin garin ke gudun hijira saboda jin ta bakinsu.
Jami'in watsa labaru na karamar hukumar Gamboru Ngala yace sun ji dadi da labarin sake kwato garinsu. Garin wani wurin kasuwanci ne babba. Ta garin ne kayan dake tashi daga Asiya ko Senegal da wasu wurare suke bi, wato akwai babbar kasuwar kasa da kasa a garin.
Kawo yanzu shekara daya ke nan da 'yan Boko Haram suka tarwatsa garin. Wasu 'yan garin sun gudu zuwa Chadi ko Kamaru da ma wasu wuraren..
Ga rahoton Haruna Dauda Biu da karin bayani.