Makon jiya ne shugaban kasar Chadi Idris Deby ya sanarda duniya cewa kungiyar Boko Haram ta samu sabon shugaba wanda ya maye gurbin Abubakar Shekau.
Kodayake sanarwar bata ambaci rasuwar Abubakar Shekau ba ana kyautata zaton rashin daidaito ne ya kunno kai har kungiyar ta zabi wani shugaban waanda watakila ka iya neman sulhu da gwamnatin Najeriya.
Kungiyar Boko Haram ta kwashe shekaru shida tana aiwatar da ta'adanci a arewacin Najeriya musamman arewa maso gabas.
Kafin ta fara kai hare-hare a kasashen dake makwaftaka da Najeriya irinsu Nijar, Kamaru da Chadi kungiyar ta kashe dubban 'yan Najeriya musamman a jihohin Adamawa, Borno da Yobe. Wasu jihohin kamar su Kano, Bauchi, Gombe, Filato, Kaduna, Nasarawa da Abuja kanta basu tsira ba.
A wani faifan bidiyo da ya fitar ranar Asabar da ta gabata Abubakar Shekau ya musanta batun cewa ya mutu ko kuma an kawar dashi daga shugabancin kungiyar.
Abubakar Shekau ya kira Idris Deby makaryaci. Shugaba Buhari kuma kafiri domin ya rungumi tafarkin mulkin dimokradiya ba na Allah ba. Saboda haka kungiyarsa zata cigaba da yaki da gwamnatin Najeriya domin Allah su ke yiwa yaki.
Bidiyon yace sako ne ga yahudawa da kiristoci da musulman da ya kira munafukai da suke cikin yaudarar kafirai. Ya yabawa shugaban kungiyar ISIS wadda ta yi ikirarin kafa daular Islama a wasu bangarorin kasashen Iraqi da Syria
Tambaya nan ita ce ina shugaba Idris Deby ya samu tabbacin an sake shugaban kungiyar. Kamata yayi ya yiwa duniya bayani akan wannan alamari dake da daurin kai.
Ga faifan bidiyon.