Yayin da India ta kaddamar da shirin bada riga kafin a kasar adadin mace-mace a kasashen duniya ya zarta miliyan biyu.
Hukumar lafiya ta duniya ta WHO za ta tura wata tawagar kwararru na kasa da kasa China a wannan makon don binciken yadda cutar coronavirus ta samo asali.
Hukumomi suna can suna ci gaba kokarin gano musabbabin abin da ya yi sanadin faduwar wani jirgin saman kasar a karshen mako da ya gabata.
Sama da ‘yan gwagwarmaya 50 aka kama a birnin Hong Kong saboda sun saba wata sabuwar dokar tsaro ta birnin.
Kasar Birtaniya ta fara bada riga kafin cutar coronavirus na kamfanin magungunan AstraZeneca ranar Litinin 4 ga watan Janairu.
Sojojin Syria sun ce Isra'ila ta harba makamai masu linzame a kusa da birnin Damascus har sojan Syria daya ya mutu.
An yankewa wata ‘yar jarida ‘yar kasar China hukuncin zuwa gidan yari tsawon shekara 4 saboda yadda ta bada rahotanni kai-tsaye daga Wuhan a lokacin da aka samu bullar annobar COVID-19.
Jiya Talata Hukumar zartarwa ta Tarayyar Turai EU - ta ba da shawarar kasashen EU su dage takunkumin tafiye-tafiye da aka kakaba wa Birtaniyya don kauce wa katse hanyoyin samar da kayayyaki da makalewar matafiya.
Yayinda kamfanoni ke tsere don ƙirƙirar rigakafin COVID-19 da ƙasashe ke warwason tabbatar da samu, wasu tambayoyi sun bullo game da amfani da kayayyakin alade a yin rigakafin.
A jiya Asabar Firai ministan Birtaniya Boris Johnson ya sanya dokar hana zirga zirga a Ingila, inda ya janye aniyar sa ta sassauta matakan kullen a lokacin bukin hutun Krismeti, bayan da aka gano sabuwar nau’in coronavirus da ta kunno kai a cikin kasar.
Sama da mutane miliyan 75 suka kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya a cewar cibiyar da ke bin diddigin annobar coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins ranar Asabar 19 ga watan Disamba.
An kara samun shugaban kasa da ya kamu da annobar Korona bairos.
Domin Kari