Lauyan da ke kare 'yar jaridar ne ya fadi haka a yau Litinin, kusan shekara daya bayan da aka samu bullar bayanan wata cuta mai shafar numfashi da ba a sani ba a tsakiyar birnin na China.
Zhan Zhan, wadda lauya ce a a baya, an yanke mata hukuncin ne a wani dan takaitaccen zama da aka yi a kotun Shanghai saboda zargin ta da tsokano fada da haddasa tashin hankali a rahotannin da ta bada a farkon lokacin da ake cikin rudanin bullar cutar ta COVID-19.
An yada rahotannin da ta bada kai-tsaye da kuma rubuce-rubucen da ta yi a kafafen sada zumunta sosai a watan Fabarairu, abinda ya ja hankalin hukumomi, wadanda suka hukunta wasu masu kwarmata bayanan coronavirus su 8 ya zuwa yanzu.
China ta yaba da yadda ta sami nasarar shawo kan annobar a kasar, ga tattalin arzikinta na farfadowa yayin da galibin kasashen duniya ke fama da matakan kulle masu zafi.
-AFP