Dakatar da hana tafiye-tafiyen ya fara ne tun ranar Lahadi, a wani yunkuri na dakile yaduwar COVID-19 da ke ci gaba a Biritaniya.
A wani bangare na shawarwarin, hukumar ta shawarci kasashe mambobin kungiyar da su hana yawan tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa da dawowa daga Biritaniya, amma ta ce ya kamata a bar mutanen da ke zuwa kasarsu ta asali yin hakan, matukar sun yi gwajin COVID-19 ko kebewa na kwanaki 10.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Shari'a na Turai Didier Reynders ya ce ya kamata kasashen mambobin su dauki matakan hada kai don hana tafiye-tafiye marasa mahimmanci, amma "hana tafiye-tafiyen bai kamata ya hana dubban 'yan EU da U.K. komawa gidajensu ba."
Kasar Jamus dake rike da mukamin shugabancin kungiyar Tarayyar Turai na karba-karba, ta tuntubi jami’an kungiyar kasashen Turan a ranar Litinin tana bukatar ingantattun tsare tsare na magance matsalolin tafiye-tafiye game da Birtaniya da kuma sabon nau’in COVID-19 da aka gano a kasar.
A makon da ya gabata ne dai Birtaniya ta gano sabon naur’in cutar kana tana aiki tare da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO. Da farko ana tunanin sabuwar cutar na yaduwa cikin gaggawa fiye da cutar ta farko, amma jami’ain hukumar WHO sun fada a wani taron manema labarai a ranar Litinin cewa babu shaidar dake tabbatar da sabon nau’in cutar na hadari ko kisa fiye da ta farko.