Tauye ‘yancin fadin albarkacin baki ne dokar hana zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a wasu sassan Jamus in ji magoya bayan Falasdinawa da ke kasar.
Dozin-dozin din dogayen motoci sun kwashe kwanaki a kusa da Rafah suna dakon a bude bodar don shigar da kayayyakin agaji cikin Gaza mai mutum sama da miliyan biyu.
A yau Asabar motocin kungiyar agajin Red Crescent ta Masar guda 20 dauke da kayan agajin jinkai da suka hada da abinci, magunguna, da ruwa sun fara shiga yankin zirin Gaza da aka yi wa kawanya ta mashigar Rafah da ke karkashin ikon Masar.
“Har yanzu akwai wasu Amurkawa akalla goma da ba a san inda suke ba, mun kuma san cewa wasu daga cikinsu Hamas na rike da su hade da wasu mutum akalla 200.” In ji Blinken.
Biden ya ce “tarihi ya nuna cewa idan ba a ladabtar da ‘yan ta’adda ko masu mulkin kama karya ba, za su iya kara haifar da rudani da mace-mace da barna.”
A Tel Aviv, shugaban Amurka Joe Biden ya dora alhakin fashewar da auku a Asibitin Gaza a kan dayan bangaren.
‘Yan Gaza da rikici ya rutsa da su a inda suke aiki a wasu garuruwa sun shiga cikin zullumi yayin da iyalensu suke kokarin kare kansu daga harin boma-bomai.
Shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Isra'ila da Jordan ranar Laraba domin ganawa da shugabannin Isra'ila da na Larabawa, yayin da ake fargabar cewa yakin Isra'ila da Hamas zai iya kazance wa ya mamaye yankin.
Dubban jama'a ne a wata unguwar Falasdinawa da ke birnin Chicago a ranar Litinin suka gudanar da jana’iza da karrama wani yaro Musulmi dan shekara 6 da aka kashe a wani yanayi da ake zargi na nuna kyamar Musulunci ne.
Masu zanga-zangar nuna goyon-bayan Falasdinawa sun karade manyan birane Landan domin neman duniya tayi adalci kan luguden wutar da ake yi a Gaza.
Yayin da Isra'ila ke shirin kai gagarumin farmaki ta kasa a gaza, akalla Falasdinawa miliyan daya da suka rasa matsugunansu na fuskantar rikicin jinkai.
Yayin da aka shiga mako na 2 da barkewar sabon fada tsakanin Isra’ila da Hamas, Zauren Malaman Addinin Musulunci na Najeriya ya bayyana rashin jin dadi kan abubuwan dake faruwa a can, a hannu guda kuma masana sun ce rashin mutunta kudurorin majalisar dinkin duniya suka sa yakin ke ci gaba da faruwa.
Domin Kari