Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Haramta Zanga-Zanga A Wasu Sassan Jamus - Magoya Bayan Falasdinawa


 Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz
Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz

Tauye ‘yancin fadin albarkacin baki ne dokar hana zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a wasu sassan Jamus in ji magoya bayan Falasdinawa da ke kasar.

Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa ta karade manyan biranen Jamus tun bayan barkewar rikici a tsakanin Isra’ila da Kungiyar Hamas da ya lakume dubban rayuka, mahukuntan Jamus dai sun ce, sun dauki matakin hana zanga-zangar a sakamakon barazanar da take yi wa tsaron kasar.

Sai dai masu zanga-zangar sun ce, shiri ne kawai na hanasu ‘yancin fadin albarkacin baki.

Kwanaki biyar da barkewar kazamin rikici a tsakanin Isra’ila da Hamas, aka soma ganin gangami na nuna goyon bayan Falasdinu a wasu sassan kasar Jamus, zanga-zangar dai ana shiryata a matsayin ta lumana.

Amma a baya-bayan nan ta kan rikide zuwa tarzoma, artabu a tsakanin jami’an ‘yan sanda da masu zanga-zangar da ake zargi da furta kalaman kyamar Yahudawa a birnin Berlin, lamarin da ya sa gwamnatin Jamus ta dauki matakin haramta duk wani gangami makamacin hakan a yanzu.

Sabuwar dokar dai ta janyo martani daga masu goyon bayan Falasdinu da ke ganin zanga-zangar ce dama daya tilo ta jan hankalin duniya kan abin da ke faruwa a zirin Gaza.

"Manyan kasashen duniya na nuna goyon baya ga Isra’ila amma ba a yarda Falasdinu ta nuna damuwa ko sukar rashin adalcin da ake mata ba, misali, kalli rikicin Rasha da Ukraine, duniya ta amince Ukraine ta kare kanta daga mamaya Rasha don tsare kasarta amma ba a yarda Falasdinu ta yi hakan ba ina adalci a nan’’ In ji Ameer Ali, daya daga cikin masu wannan tunanin…

Rana a nata bangaren na ganin ba duk aka hadu aka zama daya ba, duk da cewa an sami barkewar rikici a yayin zanga-zangar ya kamata gwamnatin Jamus ta mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki a kowanne batu da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya ba tare da ana nuna banbanci ba

"Dubban fararen hula na cikin ukuba a Gaza kuma Isra’ila ta ce za ta kai wasu sabbin hare-haren bam a arewacin Gaza, shi ya sa muke son mu fito mu ci gaba da jan hankalin duniya kan a dakatar da fadan ta hanyar wannan zanga-zangar ta lumana da muke.’’ ta ce.

Duk da dokar akwai wadanda suka yi fatali da ita suka kumą fito doń yin boren, mutum fiye da dari aka kama bisa laifin take dokar a Berlin fadar gwamnatin kasar ta Jamus.

Ayman Mazyek shugaban wata babbar Cibiya ta Musulmai mazauana Jamus a tattaunawa da kafar talabijin ta TagesThemen a Jamus ya ce, babu shakka rikicin da ke faruwa abu ne mai sosa rai, amma ya kamata kowa ya sani cewa addinin Islama bai amince da duk wani yanayi na aibata Yahudawa ko tayar da zaune tsaye ba.

"Ya ce muna son fayyacewa duniya cewa, haramun ne a addinin Islama Musulmi ya aibata ko nuna kyamar Yahudawa ko wulakanta addinin wasu, saboda haka, ba ma goyon bayan masu wannan akida a matsayinmu na Musulmi da ke nan Jamus muna Allah-wadai da yin hakan’.’

Haramta zanga-zangar ta biyo bayan wani mummunan artabu a tsakanin jami’an ‘yan sanda da masu zanga-zangar da aka samu na furta kalaman kyamar Yahudawa a yayin gangamin na birnin Berlin a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wannan al’amari ana ganin zai iya tayar da wutar rikici a kasar idan har ba a gaggauta yi wa tufkar hanci ba.

Sai dai kuma batun ya haifar da mahawara a cikin kasar kan sahihancin ‘yancin fadin albarkacin baki a Jamus.

Rikicin ya barke tsakanin Isra'ila da Hamas ne a ranar 7 ga watan Oktoba bayan d amayakan Hamas suka kai wani hari cikin Isra'ila da ya halaka daruruwan Yahudawa fararen hula.

Ba tare da bata lokaci ba Isra'ilan ta mayar da martani kan yankin Gaza lamarin da ya haddasa mutuwar dubban mutane.

Saurari rahoton Ramatu Garba Baba:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG