Kakakin dakarun Isra’ila na zargin Hamas da yin amfani da fararen hula a matsayin makari, yana mai jan kunnen al’umar yankin da su tattara su koma kudancin Gaza. Amma Hamas ta ce duk farfaganda ne.
A ranar Juma’a Shugaba Joe Biden ya gana da iyalan Amurkawan da suka bata kana ya tattauna da iyalan wadanda Hamas take rike da su.
Hamas ta yi watsi da gargadin na Isra’ila wanda ta kwatanta a matsayin farfaganda.
Dubun dubatan Musulmi ne suka yi gangamin nuna goyon bayan Falasdinu bayan kammala Sallar Juma’a a sassan yankin Gabas ta Tsakiya.
Yankin na Gaza na karkashin kawanyar Isra’ila, wani mataki da Isra'ilan ta dauka a matsayin martanin mummunan harin da Hamas ta kai wa Isra’ilan a ranar Asabar din da ta gabata, wanda ya halaka daruruwan fararen hula.
A yayin da ake murnar zagayowar ranar ‘ya’ya mata ta duniya, iyaye mata, dalibai, malamai da wasu masu ruwa da tsaki sun sake jaddada mahimmancin bai wa ‘ya’ya mata irin damammakin da ake bai wa takwarorinsu maza.
Masana sun bayyana cewa rikicin Isra’ila da Hamas ka iya sa ‘yan Najeriya fuskantar kalubale wajen sayen man fetur duk da cewa an sami hauhawar farashin man fetur a duniya, lamarin da ya kamata a ce ya taimaka wa masana’antar danyen mai ta kasar.
Shugaban Turkiyya ya bayyana cewa jirgin yakin ruwan zai haifar da mumunar barna a Filasdinu.
Hukumar kula da lafiya ta duniya ta ware ranar 10 ga watan Oktoba na kowace shekara a matsayin ranar kula da lafiyar kwakwalwa ta duniya domin wayar da kan al’umma kan abunda suka shafi kula da lafiyar kwakwalwa.
Ganin cewa rikicin na gabas ta tsakiya sai ƙara rincaɓewa yake yi, masana a Najeriya sun yi kira ga shugabanin Afirka da su yi azama wajen ganin cewa an kawo ƙarshen rikicin ba da daɗewa ba.
A yau Talata Isra'ila ta kai munanan hare-hare ta sama babu kakkautawa a zirin Gaza.
Masu sharhi kan fitinar da ta barke tsakanin Isra'ila da 'yan Hamas na karfafa tunanin cewa Majalisar Dinkin Duniya ce ke da hakkin shiga tsakani don kawo karshen wannan yaki da samun zaman lafiya.
Domin Kari