Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Saki Amurkawa Biyu – Isra’ila


Amurkawa biyu da Hamas ta sako, mahaifiya, tsakiya da 'yarta, hagu
Amurkawa biyu da Hamas ta sako, mahaifiya, tsakiya da 'yarta, hagu

“Har yanzu akwai wasu Amurkawa akalla goma da ba a san inda suke ba, mun kuma san cewa wasu daga cikinsu Hamas na rike da su hade da wasu mutum akalla 200.” In ji Blinken.

Gwamnatin Isra’ila ta ce Hamas ta saki wasu Amurkawa biyu a ranar Juma’a wadanda suna daga cikin mutanen da kungiyar ke rike da su tun bayan harin da Hamas din ta kai na ba-zata a Isra’ila makonni biyu da suka gabata.

Amurkawan wadanda suka hada da wata mata da ‘yarta matashiya wadanda asalinsu ‘yan Isra’ila ne, na daga cikin mutanen farko da aka sako.

Akwai akalla mutum 200 da har yanzu Hamas din ke rike da su.

Hamas ta ce ta mika mutanen biyu ga gwamntin Qatar bisa dalilai da suka shafi lamari na jin-kai.

A nan birnin Washington, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi lale marhabin da sako Amurkawa yana mai cewa:

“Har yanzu akwai wasu Amurkawa akalla goma da ba a san inda suke ba, mun kuma san cewa wasu daga cikinsu Hamas na rike da su hade wasu mutum akalla 200.” In ji Blinken.

Sauran ‘yan uwan wadanda ake rike da su sun nuna farin cikinsu ga wannan sabon al’amari suna masu kira da su ma a saki nasu ‘yan uwan.

Hakan na faruwa ne yayin da Shugaban Amurka Joe Biden ya mika bukatar neman dala biliyan 61.4 ga majalisar dokokin kasar don bai wa Ukraine a matsayin tallafin a yakin da Rasha ke yi da ita.

Tallafin na dauke da wani kaso na biliyoyin daloli da za a samar da makaman soji da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon za ta mikawa Ukraine da kuma tallafawa kasar a fannin tattalin arziki da ‘yan gudun hijirar Ukraine da ke zaune a nan Amurka.

Babu dai tabbacin ko majalisar dokokin Amurkar za ta amince da wannan bukata ta Biden wacce za ta ci akalla jimullar dala biliyan 105, ciki har da wani kaso da za a ware wa Isra’ila da kuma samar da tsaro akan iyakar Amurka.

Majalisar Wakilan Amurka na cikin wani yanayi na rudani yayin da ‘yan Republican da ke da rinjaye suka gaza zaban sabon Kakakin majalisar.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG