Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Motocin Agaji Sun Fara Shiga Zirin Gaza Ta Mashigar Rafah


Mashigar Rafah
Mashigar Rafah

A yau Asabar motocin kungiyar agajin Red Crescent ta Masar guda 20 dauke da kayan agajin jinkai da suka hada da abinci, magunguna, da ruwa sun fara shiga yankin zirin Gaza da aka yi wa kawanya ta mashigar Rafah da ke karkashin ikon Masar.

A wani taron kolin samar da zaman lafiya a birnin Al-Kahira a yau Asabar, Sakatare-Janar din Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fadi cewa akwai bukatar motocin agajin su yi hanzarin kai kayayyakin lami lafiya daga Masar zuwa Gaza.

Ya kuma godewa Masar saboda rawar da ta taka wajen taimakawa kai agajin.

"Amma al'ummar Gaza na bukatar a ci gaba da kai karin agajin, iya adadin da ake bukata," a cewarsa. Ya kara da cewa, "Muna aiki ba dare ba rana da duk bangarorin da suka dace don ganin hakan ya faru."

Antonio Guterres
Antonio Guterres

Jerin manyan motoci sun kwashe kwanaki da dama a kusa da mashigar Rafah suna jira a bude iyakar don kai agaji ga mazauna Gaza su fiye da miliyan biyu.

A cikin wata sanarwa shugaban hukumar kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths, ya tabbatar da cewa kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar da Majalisar Dinkin Duniya sun samar da motocin kayayyakin jinkai da ake matukar bukata. Ya ce an amince su tsallaka zuwa Gaza kuma kungiyar agajin Red Crescent ta Falasdinu za ta tarbe su, tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya.

Motocin agaji
Motocin agaji

Ayarin motocin shi ne na farko da aka ba izinin shiga Gaza ranar Asabar tun bayan da kungiyar Hamas ta kaddamar da harin ba-zata a kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 1,400, lamarin da ya sa Isra’ila kai farmaki da kuma yi wa Gaza kawanya. Falasdinawa sama da 4,000 aka kashe.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG