Hukumar Alhazai ta kasa ta ce za ta hada kai da hukumomin Alhazai na jihohi wajen jan hankalin maniyata kan sabbin tsare-tsare da kasar Saudi Arabiya ta bullo da su, domin gudanar da aikin hajjin shekara mai zuwa.
Makarantar wacce ake kira Al Fakhoura da ke Gundumar Jabalia na dauke da dubban mutane a lokacin da aka kai harin kamar yadda Juliette Touma, Darekta a hukumar ‘yan gudun hijirar ta fadawa Reuters.
Gungun ‘yan kasar waje na farko da suka makale a yankin Gaza tun bayan barkewar rikicin sun fara shiga Masar a ranar Laraba da wasu da yawa kuma a ranar Alhamis.
Yayin da sojojin Myanmar suke ci gaba da yaki da 'yancin fadi sonka, sojojin kasar ta Myanmar, sun bayyana kama wani tsohon ministan yada labarai a kasar.
China ta sanar cewa shugabancin jam'iyyar kwaminis na da mahimmiyar rawar da zai iya takawa a game da al'amuran kudade, a wurin babban taron da aka shirya don tattauna batutuwan da suka shafi samar da kudade da kuma kashe su wanda akayi a babban birnin kasar, Beijing
Amurka Ta Kara Tura daruruwan dakarunta a yankin Gabas Ta Tsakiya.
Yayin da Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Olaf Scholz da tawagarsa suka kai ziyarar aiki Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sauya Najeriya daga kasa mai rarrafe izuwa kasa mai dimbin ci gaba.
Babban Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma kai ziyarar ba-zata a Doha babban birnin Qatar a ranar Asabar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron yanayi da za a yi a Nepal.
Kakakin rundunar sojan Isra'ila ya ce har yanzu dakarun kasar na a fagen daga bayan hare-hare ta kasa da suka kai a cikin dare a zirin Gaza.
Kutsa kai da Isra'ilan take shirin yi cikin yankin na Gaza mataki ne na zakulo mayakan Hamas don mayar da martani ga mummunan harin da suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba
Jakadan Falasdinu a Najeriya, Abdullah Shawesh, ya ce cikin wadanda ke gwagwarmayar kwato wa Falasdinawa hakkinsu akwai mabiya addinin kirista da ma Yahudawa.
A ranar Juma’a mayakan na Hamas suka fara sakin wasu ‘yan Isra’ila biyu – wata mata da diyarta, kusan makonni biyu bayan da suka kai wani harin ba-zata da ya kashe Isra’ilawa sama da 1,400 mafi akasari fararen hula.
Domin Kari