Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Ta Kai Hari A Hanyoyi Da Maboyar Mayakan Hamas Na Karkashin Kasa A Zirin Gaza


Israel-Palestinians
Israel-Palestinians

Kakakin rundunar sojan Isra'ila ya ce har yanzu dakarun kasar na a fagen daga bayan hare-hare ta kasa da suka kai a cikin dare a zirin Gaza.

Jiragen yakin Isra'ila sun jefa bama-bamai a maboyar Hamas da ke karkashin kasa a arewacin zirin Gaza, a cewar jami'an sojan kasar a safiyar Asabar, a zaman wani bangare na fadada hare-hare ta kasa da ta sama da su ke kai wa domin kawar da yankunan da ke karkashin ikon mayakan Hamas, bayan harin da mayakan suka kai a kudancin Isra'ila makonni uku da suka wuce.

Rundunar tsaron Isra'ila ta ce jiragen yakinta sun kai hari a wurare da yawa a karkashin kasa sun kuma lalata muhimman cibiyoyin sadarwa, lamarin da ya janyo katsewar hanyoyin sadarwa kusan gaba daya ga al'ummar Gaza kimanin miliyan 2.3.

“Muna samun ci gaba a matakan yakin. A daren jiya, dakarun Isra’ila sun shiga zirin Gaza sun kuma fadada kai hare-harensu ta kasa," a cewar Rear Adm. Daniel Hagari kakakin rundunar a safiyar Asabar.

Hagari ya kara da cewa "har yanzu dakarun suna nan a fagen daga.

Ya kuma ce Isra'ila za ta bar manyan motoci dauke da abinci, ruwa, da magunguna su shiga Gaza ranar Asabar, abin da ke nuna yiwuwar tsagaita wuta a kai hare-haren bama-baman, akalla a kan iyakar kasar da Masar, ta inda ake shigo da kayan jinkai.

"A cikin dare, jiragen yakin rundunar tsaron Isra’ila sun kai wa Asem Abu Rakaba hari, shugaban sashen kula da jiragen sama marasa matuki da na’urorin kariya ta sama na kungiyar Hamas," a cewar jami’an rundunar tsaron ta shafin X (Twitter), abin da ke nuna cewa ta yiwu an kashe babban hafsan mayakan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG