ABUJA, NIGERIA - Cikin sabbin tsare-tsaren akwai batun yawan kwanaki da za a yi wajen bada biza ga maniyatan. Saudi Arabiya ta ce dole ne a ba duk wani maniyaci biza kwanaki 60 kafin ranar Arafa, wanda ya banbanta da yadda ake yi a shekarun baya.
Babban sakataren hukumar Alhazai ta kasa Dr. Abdullahi Rabi'u Kontagora, ya ce dole ne humukar Alhazai ta hada gwiwa da hukumomin Alhzan jihohi wajen wayar da kan maniyata kan sabbin tsare-tsaren da kasar Saudi Arabia ta fito da su, kamar irin jadawalin da kasar ta ke so a bi wajen gudanar da aikin hajjin badi.
Abdullahi ya ce bana suna so su rufe biza ne kwanaki 60 kafin ranar Arafa , wanda ya zama sabanin abin da ake yi a baya. Abdullahi ya ce akwai bukatar a bi sako-sako, loko-loko na wannan kasa domin jan hankalin maniyata wajen kokarin su biya kudin su da wuri saboda a samu a yi aiki cikin kwanciyar hankali.
Abdullahi ya kara cewa batun yawan kudin hajji da ake korafi cewa ya yi yawa, abu ne da ya jibanci canjin kudin kasar Amurka wato dala, kuma a yanzu haka dala ta yi tsada.
Shi ma sakataren hukumar zaben jihar Nasarawa Idris Ahmed Almakura, ya tabatar cewa akwai aiki a gaban su amma za su yi kokari wajen hadawa da kwararru da masana wajen neman taimako, domin su cimma burin kai dukkan Alhazan da aka ware wa jihar Nasarawa zuwa kasa mai tsarki.
Hakazalika Abubakar Salihu na hukumar Alhazai na jihar Adamawa ya yi tsokaci cewa yawancin wadanda ke tafiya aikin Hajji makiyaya ne da manoma saboda haka, idan sun gama girbin kayan amfanin gonakin su, kuma makiyaya sun kammala aikin dabbobin su, yana fata cewa zuwa karshen shekara za a samu mutane da dama da za su yi ribibin biyan kudin kujarar Makkah. Salihu ya ce kudin ne ya ke ba mutane tsoro amma kuma akwai wadanda za su cike gurbi da izinin Allah.
Abin jira a gani shi ne irin kokarin da hukumar Alhazai da ma na jihohin za su yi wajen ganin an kai Alhazan Najeriya dubu 95 zuwa kasar Saudi Arabiya, duk da wannan tsarin bada biza da kasar ta fito da shi.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna