Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mu Na Gwagwarmayar Nemar ‘Yancin Kanmu Ne - Jakadan Falasdinu A Najeriya


Abdullah Shawesh, Jakadan Falasdin a Najeriya
Abdullah Shawesh, Jakadan Falasdin a Najeriya

Jakadan Falasdinu a Najeriya, Abdullah Shawesh, ya ce cikin wadanda ke gwagwarmayar kwato wa Falasdinawa hakkinsu akwai mabiya addinin kirista da ma Yahudawa.

ABUJA, NIGERIA - Jakadan ya ce duk mai tausayi a zuciyarsa zai mara wa muradin Falasdinawa na samun kasar kansu daga mamayar Isra'ila.

"Daga 7 ga watan nan adadin wadanda su ka mutu a Gaza sun kai 5,791 inda ciki ma akwai yara 2,360, mata 1,421 da kuma tsoffi 217." Inji Jakada Shawesh a taron manema labaru a ofishin jakadancin Falasdinu na Abuja.

Ya ce "Falasdinawa 16,297 sun samu raunuka daban-daban inda fiye da 1000 ke karkashin ruguzazzun gine-gine da a ke ta famar ceto su."

Shawesh ya zayyana gwagwarmayar da su ke yi ta nemar kwatar 'yanci ce ba fadan addini ba ne kamar yadda ya ce musamman wasu mabiya addinin Kirista a Najeriya ke daukar Falasdinawa a matsayin duk Musulmi ne don su Larabawa ne, alhalin kuwa su na da mabiya addinin Kirista don cikin hare-haren Isra'ila ma ta ruguza wata tsohuwar majami'a mai tarihi a Gaza.

Shawesh ya kara da cewa kamar yadda kasashen Afirka su ka yi gwagwarmayar samun 'yanci daga 'yan mulkin mallaka, hakanan Falasdinawa ke yunkurin samun 'yanci da ya ce sun rasa tun 1948.

Jakadan ya ce duk kayan agajin da a ke shigowa da shi Gaza daga mashigar Rafa ta Masar ba su fi biyan bukatar kashi 3 na jama'ar Gaza ba.

Shawesh ya ce Najeriya na da gagarumar gudunmawar da za ta bayar wajen ciccibar neman 'yancin Falasdinawa, ya na mai gode wa 'yan Najeriya da irin goyon bayan da su ke ba wa kasarsa.

Da a ka tambaye shi ko Hamas ba 'yan bindiga ne masu saba doka da oda ba? Jakadan ya ce gasa wa Falasdinawa aya a hannu ya kawo kafuwar Hamas a 1987 inda ba kungiyar gabanin nan tun mamaye yankin Falasdinawa.

Sakataren kungiyar Kirista ta Najeriya reshen arewa ta tsakiya, Pastor Simon AS Dolly, ya ce nuna tsana ga Falasdinawa don bambancin addini ba daidai ba ne.

Hakika tattaunawa da ma muhawara mai zafi kan halin da a ke ciki a Gaza na daga manyan darussa da 'yan Najeriya ke wuni su tashi da shi inda wasu ra'ayinsu kan zo iri daya wasu kuma su yi harshen damo.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Muna Yakin Neman ‘Yancin Kan Mu Ne - Jakadan Falasdin A Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG