A ranar Talata Isra'ila da Hamas sun kusa cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta na wani dan lokaci a yakin da suke yi na tsawon makwanni shida a dalilin dimbin Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza da nufin yin musanya da Falasdinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.
Babban Malamin Addinin Musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ya bada gudummawar kudi Naira Miliyon dari (100) domin Taimaka wa Mutanen kasar Falasdinu da suke yaki da kasar Israila.
Yau Lahadi Isra’ila ta buga wani hoton bidiyo inda ta nuna wani rami da ta ce kungiyar ‘yan bindigan Falasdinu ce ta gina a karkashin asibitin Shifa dake zirin Gaza, yayin da ta maida hankali wurin nema da kuma lalata ayyukan kungiyar Hamas.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya na ziyara a Jamus domin halartar taron hadin-gwiwar Kungiyar Kasashen nan 20 masu Karfin Tattalin Arziki ta G20 da Afirka.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce “dole a kare” asibitocin da ke cikin Gaza, yayin da sojojin Isira’ila ke ci gaba da auna cibiyoyin lafiya a wannan yankin kasar ta Falasdinawa, bisa zargin cewa Hamas na rabewa da su.
Fasinjoji 87 hukumomin Saudiyyan suka amince suka shiga kasar cikin mutum 264 inda suka sa aka mayar da 177 Najeriya.
Jamus ta ce kimanin ‘yan Najeriya kimanin 12,000 da ke zama kasar ba bisa ka’ida ba ake shirin maida wa gida, hakan na zuwa ne bayan da Shugaba Tinubu ya yi na’am da bukatar a yayin wata ganawa da Shugaban Jamus Olaf Scholz a Abuja. Sai dai ‘yan Najeriyan da batun ya shafa sun ce ba zata sabu ba.
Sama da jami’an tsaro dubu uku za a baza a birnin na Paris don su tabbatar da tsaro yayin tattakin a cewar Ministan cikin gida Gerald Darmanin.
Ita dai Isra’ila ta ce Hamas na da maboya a ciki da karkashin asibitin, har ma kuma ta kafa wata cibiyar ba da umarni a karkashinsa.
Baya ga harin jirgi mara matukin na ranar Alhamis, an kakkabo sauran makaman ko kuma sun rikito da kansu a cewar Reuters.
Ofishin jakadancin kasar Canada ya dakatar da ayyukansa na wani dan lokaci biyo bayan gobarar da ta kama ofishin da yayi sanadin mutuwar mutum biyu da jikkata wasu.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, na shirin fara wata ziyara mai mahimmanci a birnin Riyad na kasar Saudiyya, a wani yunkuri na kara karfafa huldar Najeriya da kuma janyo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje.
Domin Kari