Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban ‘Yan Najeriya Marasa Takardun Zama Jamus Na Nuna Turjiya Ga Shirin Tisa Keyarsu Gida


Olaf Scholz (Photo by kola sulaimon / AFP)
Olaf Scholz (Photo by kola sulaimon / AFP)

Jamus ta ce kimanin ‘yan Najeriya kimanin 12,000 da ke zama kasar ba bisa ka’ida ba ake shirin maida wa gida, hakan na zuwa ne bayan da Shugaba Tinubu ya yi na’am da bukatar a yayin wata ganawa da Shugaban Jamus Olaf Scholz a Abuja. Sai dai ‘yan Najeriyan da batun ya shafa sun ce ba zata sabu ba.

Ziyarar Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz a Najeriya a watan Oktoban da ya gabata, za a iya cewa ta tayar da kura a tsakanin ‘yan Najeriya mazauna Jamus musamman wadanda ke zama ba bisa ka’ida ba.

Batun a tisa keyar ‘yan Najeriya kimanin dubu goma sha biyu gida ya janyo martani, inda akasarin wadanda al’amarin ya shafa ke sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan amincewar da ta yi a mayar da ‘yan kasar gida daga Jamus, ba tare da yin la’akari da wahalhalun da suka tilasta musu barin kasar don neman rayuwa mai inganci a Jamus ba.

Wasu masu neman mafaka da suka nemi na sakaya sunansu sun yi tsokaci.

"Ba abin da zai sa na koma Najeriya. A lokacin da nake Najeriya yarana ba sa zuwa makaranta mun sha kwana da yunwa, mijina ba shi da aikin yi, ga tashin hankali na rikicin kabilanci da ya tilasta mana barin kasar, gaskiyar magana ba inda zani, ba zai ma yiyu ba, zama a Jamus daram don tuni na nemi lawyan da zai tsaya mani cimma burina, a cewar wata mata da ta nemi a sakaya sunanta.'

A yayin da gwamnatin Najeriya ke cewa babu dalilin da zai sa ‘yan kasar na tserewa zuwa wata kasa har wasunsu na jefa rayuwarsu cikin hadari da zumman neman rayuwa mai inganci a kasashen waje, binciken da Muryar Amurka ta gudanar a game da wadanda ke zaune ba bisa ka’ida ba a Jamus ya gano cewa, da dama daga cikinsu sun zame wa gwamnatin Jamus jidali.

Najeriya da Jamus
Najeriya da Jamus

Wani tsohon dan gudun hijira mai suna Haruna Salisu da aka fi sani da Chizo Germany, wanda labarin hijirarsa zuwa Jamus ya dauki hankali a Jamus dama wasu kasashen Afrika, ya yi tsokaci kan halayyar wasu daga cikin ‘yan Najeriya da ake magana a kansu, da a ganinsa shi ya tunzura gwamnatin Jamus daukar wannan matakin.

Chizo ya ce yawancin mutanen Najeriya da ke zuwa kasar ba sa son aiki sai dai su karbi tallafin gwamnati.

Jamus da Najeriya sun amince da shirin fadada cibiyar nan da ake tsugunnar da wadanda ake mayar wa Najeriya daga Turai don koya musu sana’oi na dogaro da kai da sauransu, wani shiri da zai lakume makudan kudade.

Toni Tuklan, daya daga cikin shugabanin Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Jamus reshen birnin Dortmund kuma tsohon ma’aikaci a cibiyar da ke kula da kaurar jama’a, ya ce babu hikima a lamarin musamman yanzu da Jamus ke da bukatar ma’aikata da ake fatan ganin sun cike wagegen gibin da rashin ma’aikata ya haifar a kasar.

''Jamus na bukatar ma’aikata kowa ya sani, saboda haka ya kamata a tantance wadanda suka zame ma gwamnati nauyi daga wadanda suke taimaka wa kasar ta fannin aiki, musamman wadanda ba su taba aikata kowane laifi ba, me zai hana a shigar da wannan rukunin cikin tsarin kasar na koya musu sana’a daga bisani su taimaki kasar? Amma a tilasta wa mutum komawa kasar da ya gujewa bayan ya jefa rayuwarsa cikin hadari kafin ya shigo Jamus babban kuskure ne,’’ a cewar Tuklan.

Ba a dai tsayar da ranar da za a soma aikin mayar da dubban ‘yan Najeriyar gida ba, amma da dama daga cikin wadanda ake son mayarwa sun ce, yanzu suna cikin yanayi na rashin tabbas.

Saurari rahoton Ramatu Garba Baba :

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG