Gomman shugabanin Afirka ne suka isa Jamus don halartar taron hadin-gwiwar G20 da Afirka da ke mayar da hankali kan tallafawa bunkasar kasashen nahiyar Afirka da ke fama da talauci da kuma wadanda tattalin arzikin su ke bunkasa.
Najeriya ta kasance daya daga cikin wadannan kasashen da ke halartar wannan taron, wadda ake wa kallon mafi karfin tattalin arziki a nahiyar ta Afirka, sai dai wasu tsare-tsaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi, sun jefa tattalin arzikinta da na ‘yan kasar cikin matsin rayuwa.
Amma a wannan taron da za ayi a Berlin, batun kwadaita wa da jan hankalin masu zuba jari na daga cikin muhimman abubuwan da shugaba Bola Tinubu zai gabatar domin bunkasa tattalin arzikin Najeirya, kamar yadda mai magana da yawunsa Abdulaziz Abdulaziz ya shaida wa Muryar Amurka.
To ko ya ‘yan Najeriya ke kallon wannan yunkuri na shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma fatar su a gamę da taron? Tambayar kenan da wakiliyar Muryar Amurka Ramatu Garba Baba ta yi wa wasu ‘yan kasar mazauna Jamus.
Mai magana ta farko ta ce, ''Shakka babu muna bukatar shugaban kasar ya ci gaba da halartar ire-iren wadannan tarukan don samun damar bunkasa tattalin arzikin kasarmu musamman ma idan aka yi la’akari da halin da kasar take ciki, akwai bukatar a janyo hankalin masu zuba jari zuwa kasarmu tabbas’’.
Duk da wadannan mababantan ra’ayoyin da kuma shaku da ‘yan Najeriyar suke bayyanawa, mai Magana da yawun shugaban Abdulaziz Abdulaziz ya ce, sannu-sannu dai ba ta hana zuwa.
Baya ga Najeriya, akwai sauran kasashen Afirka irin su Ghana, Masar, Rwanda da dai sauransu da duk ke fatan cin moriyar wannan taro da za a kwashe kwanaki biyu ana gudanar da shi a birnin Berlin.
A saurari rahoton Ramatu Garba Baba:
Dandalin Mu Tattauna