Sannu a hankali layukan internet na kamfanonin jiragen sama sun fara dawowa yau Asabar bayan da kamfanonin sadarwa na duniya, da bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi suka fada cikin rudani sakamakon gagarumar katsewar layukan internet a cikin 'yan shekarun nan, don aikin sabunta matakin kariya.
An kashe akalla mutane 13 a wasu hare-hare uku da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke tsakiyar Gaza cikin dare zuwa yau Asabar, a cewar jami’an kiwon lafiyar Falasdinu, yayin da ake ganin ana samun ci gaba a tattaunawar tsagaita bude wuta a birnin Alkahira.
Kazalika matsalar ta shafa har da wasu kafafen yada labarai wadanda suka kasa watsa shirye-shiryensu.
Wani jirgi mara matuki kirar Iran da 'yan tawayen Houthi na Yemen suka tura a birnin Tel Aviv ranar Juma'a, ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da raunata akalla 10 a harin farko da kungiyar ta kai kan Isra'ila.
A ranar Alhamis din nan Priministan Izra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci dakarun Izra’ilan a kudancin Gaza, a yayin da tankokin yakin Izra’ilan ke kara nausawa cikin Rafah.
Sabuwar zakaran kofin kasashen nahiyar Turai ta Euro 2024 Sifaniya ta koma ta uku a jerin jadawalin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da aka fitar a ranar Alhamis, yayin da Argentina da ta lashe gasar cin kofin duniya ta ci gaba da zama a matsayi na daya bayan da ta lashe kofin Copa America.
A wani samamen kasa da kasa da ya maida hankali akan kungiyoyin batagarin dake aikata laifuffuka a nahiyoyi 5 masu tushe a kasashen yammacin Afrika, ‘yan sanda sun kama mutane 300 sun kwace tsabar kudi dala miliyan 3 da toshe asusun banki 720, a cewar rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol.
Hukumomin kasar Thailand sun bayyana a yau Laraba cewar, binciken farko da aka gudanar akan musabbabin mutuwar gawa ya nuna cewar akwai burbushin sinadarin cyanide a jinin wasu ‘yan vietnam 6 da baki Amurkawa a otel din “Central Bangkok Luxury”
Tawagar kwallon kafar Sifaniya ta lashe kofin kasashen nahiyar Turai bayan da ta ci takwararta na kasar Ingila da ci 2-1
Dr. Faruk Bibi Faruk, na jami’ar Abujan Najeriya ya ce wannan al’amari bai rasa nasaba da al’adar barin kusan kowa ya mallaki bindiga da kuma yadda siyasar Amurka ta fara daukar zafi.
A cewar jami'an binciken FBI mai kula da shiyar Pittsburgh, Kevin Rojek, hukumar bata san dalilin kai harin daya hallaka mutum guda tare da raunata wasu mutane 2 ba.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.