Gidan rediyon ma’aikatar sojan Isra’ila ta fada yau Asabar cewa sojojin Isra'ila sun auna shugaban sojan Hamas a wani hari a Khan Younis a Gaza, harin da ma’aikatar lafiyar wurin ta ce ya kashe akalla Falasdinawa 20.
Kasashen kungiyar NATO sun caccaki China, Iran, Koriya ta Arewa A Kan mara wa Rasha baya a mamayar da ta ke yi wa Ukraine.
Shahararrun ‘yan kasuwa na duniya da ‘yan siyasa sun fara hallara babban birnin kasar India a ranar Juma’a domin halartar daurin auren karamin dan Mukesh Ambani, wanda ya fi kowa arziki a Asiya.
A ranar Alhamis ne Rasha sa sanya sunan Yulia Navalnaya, wata fitacciyar yar adawa a Rasha, kuma mai dakin marigayi Alexey Navalny, kan jadawalin ta na jerin sunayen 'yan taadda da masu tsatstsauran ra’ayi.
A yau Alhamis kasar China ta zargi kungiyar tsaro ta NATO da kokarin tabbatar da tsaro ta ko wane irin hali tare da shaidawa kawancen kasashen da kada ya haddasa makamancin wannan rudani a nahiyar Asiya.
Hukumomin asibiti sun bayyana cewar, hare-haren Isra’ila takai tsakiyar zirrin gaza ta sama da sanyin safiyar yau Laraba, sun hallaka Falasdinawa 20, ciki har da kananan yara 6 da mata 3, wasunsu ma na zaune ne a wurin da sojin Isra’ilar suka ayyana da tudun mun tsira.
A yau Talata, Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya akan kare hakkin bil adama ya bayyana cewar ofishinsa na bibiyar rahotanni game da wani makeken kabari a rairayin Sahara dake kan iyakar kasashen Libya da Tunisiya bayan da a farkon shekarar nan aka gano gawarwakin bakin haure 65 a wani wuri daban
Rasha ta kai hari da makami mai linzami kan wani asibitin yara da ke babban birnin Ukraine a jiya Litinin, daya daga cikin hare-haren da ta ke kaiwa a yankunan kasar da ya wuce gona da iri, harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 31 tare da jikkata wasu 154.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a ranar Litinin ya bukaci firaministansa da ya ci gaba da kasancewa a kan mukamin a halin yanzu.
Sanarwar ta Jamus dai na zuwa ne a wani lokaci da kasar ta Nijar ta kawo karshen yarjejeniya da wasu kasashen yammacin duniya irin su Amurka da Faransa.
Sojojin Isra'ila sun zafafa wani farmaki a yanki mafi girma na yankin Zirin Gaza a wani mataki da sojojin suka ce na fatattakar 'yan ta'adda ne.
Wani babban harin makami mai linzami da Rasha ta kai a Ukraine ya kashe akalla mutum 28 tare da jikkata kusan 100 a ranar Litinin, kamar yadda jami'ai suka ce.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.