Jamus za ta ba da gudummawar alluran rigakafi 100,000 na cutar kyandar biri wato mpox daga hannun jarin sojojinta don taimakawa wajen shawo kan barkewar cutar a nahiyar Afirka na cikin kankanin lokaci tare da ba da taimako ga kasashen da abin ya shafa, in ji kakakin gwamnati a ranar Litinin.
Hare-haren 'yan awaren akan ofisoshin 'yan sanda, layin dogo da manyan tituna a Lardin Balochistan da ke Pakistan, tare da daukar fansa da jami'an tsaro suka yi, sun hallak akalla mutane 51, kamar yadda jami'ai suka sanar a ranar Litinin.
A wani jawabi da zai gabatar a ranar Talata, Starmer zai bayyana cewa "sauyi ba zai faru cikin dare daya ba" amma gwamnatinsa ta kuduri aniyar magance dimbin matsalolin da suka hada da cunkoson gidajen yari, har ya zuwa dogon jira da ake samu a sha’anin kiwon lafiya.
Tun da farko a jiya Asabar, 'yan sanda sun ce sun tsare wani matashi dan shekaru 15 da suka ce mai yiwuwa yana da alaka da harin amma suka ce ba’a kai ga kama wanda ya kitsa kai harin.
An kama Pavel Durov bisa wani bincike kan rashin masu kula da daidaita al’amura a manhajar Telegram, kuma 'yan sanda sun dauka cewa wannan lamarin ya ba da damar ci gaba da aikata laifuka ba tare da daukar mataki ba a manhajar ta aika saƙwanni.
Kotun kolin Venezuela, wadda ake yiwa kallon ‘yar amshin shatar Maduro, a ranar Alhamis ta tabbatar da sake zabensa a wani wa’adin mulki na 3 mai tsawon shekaru shida, tare kuma da tuhumar Gonzalez Urrutia kan kin bayyana kamar yadda aka umarce shi.
Jami'an 'yan sanda na musamman sun shiga aikin farautar wani mutum da ba a san ko su wanene ba, wanda ya kai hari da wuka a wani wajen taron jama'a a birnin Solingen da ke yammacin Jamus, inda ya kashe mutane uku tare da jikkata wasu akalla takwas, biyar daga cikinsu sun sami munanan raunuka.
Masu zanga-zangar na nuna bacin ransu kan yunkurin da 'yan majalisar dokokin kasar da abokan shugaba Joko Widodo suke yi na neman sauya tsarin zabe ta yadda zai amfane su.
Ziyarar ta Modi ta zo ne bisa gayyatar Zelenskyy, wanda ya nuna fushin sa kan ziyarar da Modi ya kai Moscow a farkon watan jiya.
Kusoshin jam'iyyar Democrat da dama sun yi jawabai a rana ta uku a babban taron kasa na jam'iyyarsu wanda ke gudana a birnin Chicago na jahar Illinois ta Amurka
Ukraine ta kai wani babban hari a birnin Moscow a ranar Laraba tare da harbo jiragen sama mara matuka guda 11 da jami'an tsaron kasar Rasha suka ce na daya daga cikin hare-hare mafi girma na jirage marasa matuka akan babban birnin kasar tun bayan yakin na Ukraine da aka fara a watan Fabrairun 2022.
Hukumomin mulkin sojan Burkina Faso, Mali da Nijar sun rubutawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wasika domin yin Allah-wadai da zargin goyon bayan da kasar Ukraine ke yi wa kungiyoyin 'yan tawaye a yankin Sahel da ke yammacin Afirka, kamar yadda kwafin wasikarsu ta nuna.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.