Shahararren dan wasan kwallon kafa din nan, Cristiano Ronaldo, na cikin matukar bakin ciki sanadiyyar rasa daya daga cikin 'yan tagwayensa.
Tuni hukumar kwallon kafar kasar ta NFF ta janye kwantiragin shekara biyu da rabi da ta ba Eguavoen, kana ta rusa tawagar masu horar da kungiyar ta Super Eagles.
Ghana ta samu wannan dama ce saboda ta bi Najeriya har gida ta zura mata kwallo daya.
A watan Fabrairu ‘yan wasan suka hadu a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika da Kamaru ta karbi bakunci, inda Senegal ta doke Egypt.
Wannan shi ne karo na shida a jere da Barcelona take kaucewa shan kaye a wasan na ‘El Clasico.’
Kididdiga ta nuna cewa cikin minti 16 Benzema ya zura duka kwallayen ukun a ragar Paris Saint Germain.
Nan da kwana 20 ‘yan wasan Rashar za su kara da Poland a wasannin shiga gasar wacce Qatar za ta karbi bakunci a bana.
Ana kara saka takunkumi akan ‘yan wasan Rasha a wasanni daban-daban da ake yi a sassan duniya a daidai lokacin da mai kulob din Chelsea ya saka ta a kasuwa.
“A yau, ba za mu lamunci matakin da FIFA ta dauka ba (kan Rasha)” Shugabar hukumar kwallon kafar kasar Poland, Cezary Kulesza ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Dan wasan PSG Neymar ya ce yana taya 'yan kasar tasa da addu'ar samun mafita yayin da suke cikin wannan hali.
Baya ga wasan na Atletico da United, Benfica za ta karbi bakuncin Ajax a wasa na biyu da za a buga a wannan Laraba.
Kocin kungiyar Unai Emery zai yi Rashin dan wasa Gerard Moreno, amma kuma zai iya dogaro da Arnaut Danjuma, wanda ya zura kwallaye 8 a gasar La Liga a wannan kakar wasa.
Domin Kari