Kamar yadda ta saba, Najeriya ta sake burgewa a idon duniya, bayan da 'yar kasar, Tobi Amusan, ta sake ba da marada kunya a fagen daga amma na wasanni.
Kasar Morocco mai masaukin baki ta lallasa Najeriya mai rike da kofi a kwallon kafa na matan Afurka. Amina Seyni ta Nijer mai sheka gudun nan ta sake ba su mamaki.
Kasashen Australia da New Zealand ne za su karbi bakuncin gasar ta cin kofin duniya ta mata a badi.
Yau fagen labaran wasannin, a maimakon labarin shahara a fafatawar da ake yi kawai, zai fi mai da hankali ne kan shahara wajen mallakar dukiyar da ake samu wajen daya daga cikin wasannin, wato Golf.
Yayin da matan Turawa ke can Ingila su na gwabzawa a gasarsu ta Turai, a Afurka ma ana nan ana kan fafatawa a matakai daban daban na wasanni iri iri.
Ana fatan za a kammala cinikin dan wasan gabanin kungiyar ta Chelsea ta fara rangadin wasannin ta da tsimi da za ta yi a kasar Amurka kafin a fara sabuwar kakar wasa.
Wilshere ya yi ritaya ne a ranar Juma’a bayan raunin da ya samu wanda ya haifar masa da cikas ga rayuwarsa ta taka leda.
Domin Kari