Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tawagar ‘yan wasan Super Falcons ta mata murnar samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
‘Yan wasan na Najeriya sun samu gurbin ne bayan da suka doke Kamaru da ci 1-0 a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka ta mata da ake wa lakabi da WAFCON wacce ke wakana a kasar Morocco.
A daren ranar Alhamis, Super Falcons wacce sau tara tana daukan kofin, kuma a yanzu ita take rike da shi, ta doke Kamaru.
“Shugaba Buhari ya yi matukar yaba irin rawar da tawagar ta taka a wannan gasa da kuma yadda ta ci gaba da rike kambunta a matsayin zakara.” Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin Buhari, Femi Adesina ta ce.
Fadar ta shugaban kasa ta kuma yi fatan tawagar ‘yan wasan ta Super Falcons, za ta taka rawar sama da wacce ta taka a gasar cin kofin duniya ta mata a 2019, inda ta wuce matakin rukunin farko a karon farko cikin shekaru 15.
Kasashen Australia da New Zealand ne za su karbi bakuncin gasar ta cin kofin duniya ta mata a badi.