‘Yar Najeriya Tobi Amusan ta kafa sabon tarihi na duniya ta wajen kammala tseren gudun fanfalaki na mita 100, inda kuma ta lashe lambar zinari a gasar guje-guje da tsalle-tsalle da aka gudanar a jihar Oregun ta kasar Amurka.
Amusan mai shekaru 25, ta karya lagon tarihin da Keni Harrison ta kasar Amurka ta kafa, na kammala gudun fanfalakin a cikin dakika 12 da digo 23 a shekara ta 2016, inda a yammacin jiya Lahadi ta kammala shi a cikin dakiku 12.6.
Tun da farko dai sai da ta karya tarihin bayan da ta kammala tseren na matakin kusa da na karshe a cikin dakika 12.12, to amma kuma an ki amincewa da wanda ta yi a matakin wasan karshe, saboda hukumomin shirya gasar sun ce an yi iska mai karfi a wannan lokacin, da zai iya kara gudu.
Amusan dai ta kasance ‘yar Najeriya ta farko da ta zama zakarar duniya a gasar, wadda ta farantawa ‘yan kasar da dama.
Tuni da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya yaba tare da jinjina wa ‘yar wasan, saboda nasarar da ta samu, wadda ya ce ta kara haskaka kimar Najeriya a idon duniya.
Haka su ma ‘yan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu da na PDP Atiku Abubakar da ma wasu manyan ‘yan siyasa, duk sun fitar da sanarwar yabawa da kwazon Amusan, da kuma kishin kasar da ta nuna a yayin gasar.
Ana samun rade-radin yiwuwar dan wasan PSG da Argentina Lionel Messi ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona ta kasar Spain, a yayin da aka ruwaito shugaban kungiyar Juan Laporta, yana cewa har yanzu kofar kungiyar a bude take ga komawar Messi.
Messi ya bar Barcelonar ne a bara bayan karewar wa’adin kwantaraginsa, a daidai lokacin kuma kungiyar ke fuskantar kalubalen kudi, ta yadda ba za ta iya ci gaba da biyansa ba.
Wannan ya sa ya koma PSG ta kasar Faransa, to amma har yanzu Laporta bai cire tsammanin dawowarsa Barcelona ba.
A kasar Italiya kuma a yayin da rahotanni suka bayyana cewa kungiyar Atletico Madrid na kokarin daukar dan wasan Manchester United ta Ingila, Cristiano Ronaldo a zaman aro, magoya bayan kungiyar sun nuna rashin amincewarsu kan matakin.
A ’yan kwanakin nan an yi ta baza rahotannin da ke alakanta Ronaldo da komawa Atletico din a wannan bazara, bayan da ya fito karara ya bayyana bukatarsa na barin United.
To sai dai kuma magoya bayan kungiyar sun karade kafafen sada zumunta suna kalubalantar matakin, ciki har da soke hotunansa da jan layi.
Kafin nan dai wasu manyan kungiyoyi irin su Chelsea sun yi yunkurin sayen dan wasan mai shekaru 37, to amma kuma duk daga baya suka sauya shawara.
Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna: