Tsohon dan wasan Arsenal kuma dan wasan tsakiya na kasar Ingila, Jack Wilshere ya yi ritaya yana mai shekaru 30.
Wilshere ya yi ritaya ne a ranar Juma’a bayan raunin da ya samu wanda ya haifar masa da cikas ga rayuwarsa ta taka leda.
Wilshere ya kasance dan wasa mafi karancin shekaru da ya fara takawa Arsenal leda a lokacin yana da shekara 16.
Dan wasan na daga cikin tawagar Ingila da ta je gasar cin kofin duniya a shekarar 2014, inda aka fitar da kasar a zagayen farko karkashin jagoranci Roy Hodgson.
“Na yi matukar sa’a da na samu irin wannan daukaka, amma hakan da ba za ta samu ba, in ba don irin soyayya da na samu da goyon baya daga gare ku ba.” In ji Wilshere.
Wilshere ya lashe kofin FA Cup tare da Arsenal a shekarun 2014 da 2015.
Daga baya kuma ya koma Bournemouth a matsayin dan wasan aro sannan ya koma kungiyar West Ham a shekarar 2018.
Ya kuma sake komawa Bournemouth karkashin wani gajeran kwantiragi a watan Janairun 2021.