A wani mataki na kara yawan man dake rumbunta na ajiya daga biliyan 37 zuwa 50 da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar gwamnatin Najeriya ta kaddamar da aikin tonon mai a matakin farko a yankin Ajibu wato Kayarda dake karamar hukumar Obi na jihar Nasarawa.
Tawagar dan takarar jam’iyyar PDP a babban zaben 2023 Atiku Abubakar, ta gudanar da zanga-zangar lumana zuwa hukumar zabe don nuna rashin amincewa da sakamakon zaben.
Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya jagorancin bukukuwan tunawa da ranar zagayowar 'yancin kasar, Laraba 3 ga watan Agusta a Tilbaery inda ya karrama wasu gwamnonin Jihohin Najeriya biyu da wasu manyan 'yan kasuwa soboda gudunmawar da suka bayar wajen karfafa hulda tsakanin Najeriya da Nijar.
Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan wasu masu ibada a coci sannan suka tada bam a cocin ta katolika da ke kudu maso yammacin Najeriya ranar Lahadi 5 ga watan Yuni
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya kaddamar da ayyukan hanyoyi da gadoji da sauran ayyukan more rayuwa a yankin Kafanchan dake kudancin Kaduna da kuma wasu ayyukan a kwaryar garin Kaduna, ya ce Kaduna ta canza fasali karkashin gwamna Nasuru Ahmed El-rufa'i.
Domin Kari