Haka kuma yace wajibi wadanda za su tsaya masan su mallaki filaye ko gidaje a Abuja.
Majalisar tattalin arziki ta Nigeria wadda ta kumshi dukan gwamnonin kasar ta amince da kudurin kafa’yan sandan jihohi a kowacce jihadomin tunkarar matsalolin tsaro da ya dabaibaye kasar.
Yayinda Amurka ta kashe sama da dala miliyan takwas a matsayin gudunmawa a bangaren kiwon lafiya a Najeriya, ta kara jaddada kudirinta na taimakawa wajen gina kasar a matsayin babbar kasa mai kwakkwaran tsarin kiwon lafiya, yaki da cin hanci da tabbatar da gaskiya da adalci
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana kulla yarjejeniyar yadda za ta karbi karin rancen dalar Amurka Miliyan 500, domin cimma kudirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na Renewed Hope.
Tinubu wanda ya kasance shugaban kungiyar ECOWAS, yace shugabannin kasashen 3 na jan kafa wajen samar da jadawalin mika mulki hannun farar hula da bayanannen lokaci.
Za a samu karin lantarkin ne sakamakon nasarar kammala kashin farko na shirin samar da lantarki na shugaban kasa (PPI).
Fiye da mutane dubu dari (100,000) ne suka rasa matsugunansu saboda tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi a jihar Zamfara, inda da yawa daga cikin su ke fuskantar mawuyacin hali kamar rashin abinci, kiwon lafiya, da matsuguni.
A cewar bayanan dake shafin yanar gizon ofishin jakadancin, ziyarar farko za ta kunshi “nazarin takardun da mutum ya gabatar” tare da jami’in karamin ofishin jakadancin. Ziyarar ta 2 za ta kasance ganawar neman bizar da kanta,
A cewar Sarkin babu wata sanarwa a hukumance dangane da dalilin daukar matakin.
An kama wanda ake zargin ne yayin sintirin yau da kullum akan babbar hanyar ‘Yan Tumaki zuwa Kankara a ranar 19 ga watan Nuwamban daya gabata a karamar hukumar Danmusa ta jihar.
Kamfanin yace rushewar babban layin lantarkin ta faru ne da misalin karfe 1 da mintuna 33 na ranar yau, Laraba, abin da ya sabbaba daukewar lantarki a dukkanin layukan rarraba wutar.
An ce faruwar lamarin ta haddasa gagarumin tsaiko, inda aka jinkirta tashin jirage da dama yayin da hukumomi ke kokarin yin gyara a kan titin tashin jiragen da al’amarin ya faru.
Domin Kari
No media source currently available