Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bikin Kirsimeti: Gwamnatin Kebbi Ta Baiwa Al’ummar Kirista Gudunmawar Manyan Motocin Shinkafa 3


Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris

Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya bada gudunmowar manyan motocin shinkafa 3 ga al’ummar Kirista domin tallafawa bukukuwan Kirsimeti.

Mataimakin gwamnan na musamman akan harkokin addinin Kirista, Samuel Audu Dabai, ne ya sanarda hakan a zantawarsa da tashar talabijin ta Channels a birnin Kebbi.

Dabai ya kara da cewar a bana, gwamnatin jihar ta baiwa al’ummar Kirista gagatumar gudunmowa, domin tabbatar da sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara cikin walwala.

A cewarsa, kiristoci a jihar sun kimtsa tsaf domin bukukuwan, inda da dama ke komawa Kebbi, a yayin da wasu ke balaguro zuwa garuruwansu.

Dabai ya kara cewar nan bada jimawa ba manyan motocin zasu bar Birniin Kebbi zuwa yankin kudancin jihar dake da dimbin mabiya addinin Kirista domin rabawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG