Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a unguwar Iyaganku, ta birnin Ibadan, ta ba da umarnin ajiye muhimman wadanda suke da hannu a mummunan turmutsutsin da ya faru a babbar kwalejin harkokin addinin Musulunci ta Bashorun, a makon da ya gabata, a gidan gyaran hali.
Mutanen sun hada da shugaban kwalejin, Abdullahi Fasasi da shugaban gidan rediyon Agidigbo FM, Alhaji Oriyomi Hamzat da kuma tsohuwar matar basaraken kasar Ife (Ooni na Ife), Naomi Silekunola.
Hukuncin kotun karkashin jagorancin Babban Alkalin Majistare Olabisi Ogunkanmi na zuwa ne a yau Talata, sakamakon gurfanar da mutanen da rundunar ‘yan sandan jihar Oyo tayi.
An gudanar da zaman kotun ne a bisa tsauraran matakan tsaro, inda dandazon dangi da sauran wadanda al’amarin ya shafa suka taru a wajen ginin kotun.
Mutanen dai na fuskantar tuhume-tuhume guda 4 dake da nasaba da turmutsutsin, kamar yadda jami’in dan sanda mai gabatar da kara, wanda ya kafa hujja da sashe na 324 na kundin hukunta manya laifuffuka, karamin sashe na 38 mujalladi na 2, na dokokin jihar Oyo na shekarar 2000, ya zayyano.
Bayan sauraron tuhume-tuhumen da ake yiwa mutanen, Alkalin Majistare Ogunkanmi ya ba da umarnin ajiye mutanen 3 a gidan gyaran hali na Agodi, a yayin da ake cigaba da dakon umarnin babban mai shigar da kara na jihar.
Dandalin Mu Tattauna