Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Laraba 25 ga watan Disamban da muke ciki da Laraba 1 ga watan Janairu mai kamawa a matsayin ranaikun domin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya ayyana hakan a madadin gwamnatin tarayyar kasar a sanarwar da babban sakatare a ma’aikatar, Dr. Magdalene Ajani ta fitar, ya mika sakon fatan alheri ga ‘yan Najeriya, inda ya bukacesu da suyi amfani da lokacin hutun domin yin tuntuntuni akan halayen kaunar juna da zaman lafiya da hadin kai da irin wannan lokaci ke koyarwa.
Dr. Tunji-Ojo ya kuma jaddada muhimmancin lokacin a matsayin wanda za’a bunkasa kwanciyar hankali da karfafa zumunta tsakanin iyalai da sauran al’ummar gari.
Haka kuma ministan ya nemi ‘yan Najeriya su jajirce wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya da hadin kai da cigaban kasa domin samun bunkasarta.
Dandalin Mu Tattauna