Tinubu ya gabatar da daftarin kasafin kudin 2025 na Naira tiriliyan 49.7 a gaban zaman hadin gwiwar majalisun tarayya, inda ya warewa fannonin tsaro naira tiriliyan 4.9, ayyukan raya kasa naira tiriliyan 4.06, kiwon lafiya, naira tiriliyan 2.48 sai kuma ilimi da zai ci naira tiriliyan 3.52.