Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwalara Ta Kama Fiye Da Mutane Dubu 2 Tare Da Hallaka 63 A Jihohin Najeriya 33 - NCDC


Cutar Kwalara A Kamaru
Cutar Kwalara A Kamaru

Hukumomin Lafiyar Najeriya sun bayyana cewar an samu bullar annobar kwalara har sau fiye da dubu 2, 100 a jihohin kasar 33.

A jawabinsa ga manema labarai game da matakan da ake dauka domin dakile annobar, Babban Daraktan Hukumar, NCDC, mai yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya, Jide Idris, yace adadin wadanda cutar ta hallaka ya kai kaso 3 cikin 100.

Ya kara da cewa an tattara alkaluman ne izuwa ranar 30 ga watan Yunin daya gabata.

Yace hakan wani gagarumin kari ne akan mutane dubu 1, 579 da aka bada rahoton sun kamu da cutar a mako guda daya gabata, inda yayi karin haske akan yanayin saurin yaduwar annobar.

A cewarsa, “izuwa ranar 30 ga watan Yunin daya gabata, mun samu adadin mutane 2, 102 da suka kamu da cutar sannan ta hallaka mutum 63 da jihohi 33 da kananan hukumomi 122 inda mizanin yawan kisan nata ya kai kaso 3 cikin 100”.

Dr. Jide Idris ya kara da cewa, jihohin Legas da Bayelsa da Abia da Zamfara da Bauchi da Katsina da Cross River da Ebonyi da Rivers da kuma Delta ne suka samar da kaso 90 cikin 100 na yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.

Ya kuma danganta barkewar annobar da sha da cin gurbataccen ruwa da abinci, inda yayi karin bayani akan yadda cudanyar jama’a ke taimakawa wajen yaduwar cutar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG