A bayan mummunar annobar kwalara a Najeriya, an bukaci gwamnati da ta samar da ruwan sha mai tsabta tareda hanyoyin tsabtace muhalli
Dr. Lawal Bakare na HIET Solutions yana son hada mutane dubu 300 domin su goge hakori lokaci guda, su shiga littafin tarihi na Guiness
Alamun cutar Maleriya su na fara bullowa kwanaki 10 zuwa 15 a bayanda sauro mai dauke da wannan cuta ya ciji mutum
Ana iya kamuwa da cutar Maleriya ce kawai ta hanyar cizon macen sauro da ake kira "Anopheles" watau mutum ba zai iya dauka daga wani ba
Kwayar halittar cuta ta Plasmodium wadda macen sauro ke yadawa ita ce ke janyo zazzabin Maleriya, kuma tana da jinsuna hudu
Shin ko kasan cewa a shekara ta 2008, mutane miliyan 247 suka kamu da cutar Maleriya, kusan miliyan daya daga cikinsu kuma suka mutu?
Kwararrun daga Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka sun ce ba su taba ganin inda dalma ta bata yanayi kamar a Zamfara ba a iya saninsu
UNICEF yace yin gwaji da jinyar da ta kunshi bayarda magunguna masu dakushe kaifin HIV, zasu iya hana mata masu ciki ba jariransu cutar
Masana kimiyya sun ce har kashi 73 cikin 100 na mazajen da suka yi amfani da wannan magani sun samu kariya daga kamuwa da HIV
Mutane 201 sun samu shanyewar jiki, mutane 104 kuma sun mutu a dalilin annobar cutar Polio (shan inna) da ta bulla a Kwango-Brazzaville
Kwararru sun yi kiran da a yi kokarin kawar da wannan ciwo daga duniya, amma sun ce yin hakan sai an samu maganin rigakafinsa.
Hukumomin kiwon lafiya a kasar sun ce mutane fiye da dari biyu da hamsin sun mutu, wasu fiye da dubu 3 sun kamu da wannan cuta.
Domin Kari