Yawan mutanen da cutar kwalara ta ke kashewa a kasar Haiti yana ci gaba da karuwa.
Hukumomin kiwon lafiya na wannan tsibiri sun ce mutane 253 sun mutu, wasu fiye da dubu 3 kuma sun kamu da wannan cuta mai haddasa amai da gudawa.
Damuwa tana karuwa kan cewa wannan cuta zata yadu zuwa sansanonin share-ka-zauna marasa tsabta dake kusa da Port-au-Prince, babban birnin kasar, inda daruruwan dubban mutane suka nemi mafaka a bayan girgizar kasar watan Janairu, kuma a bayan da aka gano mutane 5 dauke da wannan cuta a babban birnin.
Amma kuma babban jami'in kiwon lafiya na kasar Haiti, Gabriel Thimote, yace yawan mutanen dake kamuwa da cutar yana raguwa, kuma da alamun za a iya shawo kan yaduwar wannan cuta.
Ya zuwa yanzu dai, wannan cuta ta kwalara ta fi karfi a yankin Artibonite dake tsakiyar kasar ta Haiti, inda kuma aka fara samun rahoton bullar cutar a makon da ya shige.
A wani yunkurin shawo kan yaduwar wannan cuta, kungiyoyin agaji na kasashen waje su na rarraba kwayoyin maganin tace ruwa, da kayan tsabtace jiki, da kuma magunguna a yankunan da aka samu bullar cutar.
Cutar kwalara, wadda wata kwayar cuta ke haddasawa, ana samunta ne ta hanyar shan ruwa ko abincin da wannan kwayar cuta ta shiga ciki. Ana iya warkar da wannan cutar, amma idan ba a yi hakan ba, tana iya kashe mutum cikin 'yan sa'o'i kadan.