Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Sun Ce Gubar Dalma A Jihar Zamfara Ta Yi Yawan Da Ba Su Taba Gani Ba


Yaran da suka sha ko suka shaki gubar dalma su na jiran ganin likita a Gusau, hedkwatar Jihar Zamfara ranar 9 Yuni 2010
Yaran da suka sha ko suka shaki gubar dalma su na jiran ganin likita a Gusau, hedkwatar Jihar Zamfara ranar 9 Yuni 2010

Kwararrun da Najeriya ta gayyata daga Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka sun ce ba su taba ganin inda dalma ta bata yanayi kamar a Jihar Zamfara ba

Akasarin lokuta, gubar dalma tana janyo laulayi ne ko nakasa dake shafar wadda ta kama na tsawon rayuwa. da wuya gubar dalma ta yi kisa nan da nan. Amma wannan abin ba haka aka gani a Jihar Zamfara dake arewacin Najeriya ba, inda a cikin watanni shida kawai da suka shige, gubar dalma ta kashe yara fiye da dari hudu.

Aikin tono ko neman karfen zinare da ake yi ba bisa izni ba a wannan yanki, ya janyo fitar guba mai matukar yawa wadda ta watsu ta shiga ruwan dake wannan yanki na Jihar Zamfara.

Kwararrun lafiya a Najeriya su na binciken cutar gubar dalma a Jihar Zamfara
Kwararrun lafiya a Najeriya su na binciken cutar gubar dalma a Jihar Zamfara

A bisa rokon gwamnatin Najeriya, Cibiyar Yaki da Yaduwa da Rigakafin Cututtuka ta Amurka ta tura kwararru zuwa Jihar ta Zamfara domin su yi nazarin wannan lamarin. Kwararrun suka ce yawan gubar dalma da suka auna, da kuma fadin yankin da ta bazu, abu ne da ba su taba ganin kamar sa ba.

Kungiyoyin agajin gaggawa sun bayyana cewa su na zaton yawan yankin da wannan gubar dalma ta shafa ya zarce yadda ake tunani tun farko, haka kuma su na jin cewa yawan mutanen da suka mutu sun zarce yadda aka fada nesa ba kusa ba.

haka kuma akwai alamun cewa ruwan sama da aka yi ta samu lokacin damina, ya baza wannan guba ta dalma zuwa wurare masu yawa, ta shiga cikin ruwan shan mutane da dabbobi, ta kuma jefa rayukan wasu yaran na Najeriya cikin hatsari.

XS
SM
MD
LG