Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikakken Bayanin Cutar Maleriya Kashin Farko - Shin Ko Ka Kasan?


Irene Salama rike da 'yarta wadda ake ba wani sabon maganin gwaji na rigakafin kamuwa da cutar maleriya ko zazzabin cizon sauro a kasar Kenya.
Irene Salama rike da 'yarta wadda ake ba wani sabon maganin gwaji na rigakafin kamuwa da cutar maleriya ko zazzabin cizon sauro a kasar Kenya.

Shin ko kasan cewa a shekara ta 2008, mutane miliyan 247 suka kamu da cutar Maleriya, kusan miliyan daya daga cikinsu kuma suka mutu?

Shin Ko Ka San:

Maleriya ko zazzabin cizon sauro cuta ce dake iya yin kisa, wadda sauro ke yadawa ga mutane idan suka cije su suka sanya musu kwayar halittar dake janyo wannan cuta?

A shekarar 2008, Maleriya ta kashe mutane kusan miliyan daya, akasarinsu yara kanana a nahiyar Afirka?

Ana iya rigakafin kamuwa da cutar Maleriya, kuma ana iya warkar da ita idan ta kama mutum?

Cutar Maleriya tana iya rage kaya da ayyukan da kasa ke sarrafawa da kimanin kashi 1.3 cikin 100 a shekara idan har ta yi yawa a cikin kasar?

Baki daga kasashen da babu cutar Maleriya sun fi harbuwa da cutar idan sauro mai dauke da wannan cuta ya cije su a saboda jikinsu ba yi da kariya?

A shekara ta 2008, mutane miliyan 247 suka kamu da cutar Maleriya, kusan miliyan daya daga cikinsu kuma suka mutu. Mafi yawan wadanda suka mutu yara ne kanana a nahiyar Afirka. A nahiyar ta Afirka, cutar Maleriya tana kashe yaro guda cikin kowace dakika 45. Cutar ta Maleriya ita ce ke haddasa kashi 20 cikin 100 na dukkan mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa.

KASHIN FARKO NA CIKAKKEN BAYANIN CUTAR MALERIYA

XS
SM
MD
LG