Kungiyar masanan lafiya na Nigeriya sun yarda da matakin farko na binciken maganin rigakafi na cutar cizon sauro da aka sani da suna, PfSPZ, wanda masana suka sarrafa a kwalejin binciken cututtuka ta NIAID, wani sashi na kwalejin lafiya.
Hukumar lafiya ta duniya ta amince da amfani da maganin Isoniazid, domin yiwa masu fama da cutar kanjamau rigakafin tarin fuka amma ba a fara amfani da maganin ba a kauyuka sai bayan da aka gama wannan bincike a Johns Hopkins da Brazil.
An kiyasta cewa mutane miliyan daya da dubu dari shida suke mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar kanjamau kowacce shekara
Asusun tallafawa kananan yara UNICEF ta bayyana cewa Nigeriya tana kan hanyar shawo kan cutar ciwon shan inna.
Kimanin ‘yan Nigeriya 300,000 suke mutuwa kowacce shekara daga matsalolin rashin lafiya sakamakon kamuwa da cutar kanjamau abinda kuma yasa ake samun kimanin kananan yara marayu Bmiliyan 1.5 a shekara.
Kamfanin sarrafa magunguna na Birtaniya GlaxoSmithKline yana neman izinin sayar da allurar rigakafin cizon sauro da aka gwada a yawancin cututtukan yaran kasashen Africa.
Masana daga kasashe, ciki har da Najeriya, sun ce tilas gwamnatoci da hukumomi su dauki matakan samun yardar jama'a da kuma bada muhimmanci ga Polio a rigakafin da aka saba yi
An fara aikin rigakafin shan inna a jihar Kano dake arewacin Nigeriya. Jihar tana shirin yiwa kananan yara miliyan 3 domin kiyaye su daga cutar shan inna da kuma bakon dauro.
Kundiyar aikin jinkai ta Rotary reshen birnin tarayya Abuja ya fara yin wani shiri yaki da cutar gudawa a kauyen Deidei dake kusa da babban birnin tarayya, saboda yadda cutar take kara yawa a kauyen.
Cibiyar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA tace zata taimaka da dala miliyan biyu da rabi domin kula da lafiyar iyaye mata da kananan yara
Hukumar UNICEF ta bayyana cewa kusan kananan yara miliyan sha daya a Najeriya suna shan wuya saboda rashin abinci mai inganci.
Wani rahoton da aka yi a yi a jihar New York ya nuna cewa kwana da jarirai a gado daya da iyayensu mata, yakan taimakawa iyayensu mata shayar da su da nono har zuwa lokacin da masanan lafiya suka tsara musu
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.